Yan bindiga sun halaka wani hazikin sojan sama a Kaduna (hoto)

Yan bindiga sun halaka wani hazikin sojan sama a Kaduna (hoto)

- Yan bindiga sun halaka wani hazikin jami'in sojan sama a Birnin Gwari, jihar Kaduna

- An tattaro cewa mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba

- Bulama Bukarti, wani lauya mazaunin Kano, ya wallafa mummunan labarin a shafinsa na Twitter

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kashe wani jami’in sojan sama kuma jami’i mafi hazaka a wani darasi na musamman na rundunar sojin sama (NAF), Muhammad Auwal.

An tattaro cewa lamarin ya afku ne a Birnin Gwari, jihar Kaduna a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Babbar nasara: Yan sanda sun damke gagararrun ƴan fashi, sun kwace makamai da kuɗi

Bulama Bukarti, wani lauya mazaunin Kano, ya wallafa mummunan labarin a shafinsa na Twitter.

Yan bindiga sun halaka wani hazikin sojan sama a Kaduna (hoto)
Yan bindiga sun halaka wani hazikin sojan sama a Kaduna Hoto: Bulama Bukarti
Source: Twitter

Ya wallafa cewa: “Jami’in sojin sama Muhammad Auwal na daya daga cikin hazikan sojojin da muka rasa a hannun yan ta’adda.

"An kashe shi a ranar 5 ga watan Satumba. A bakin aiki a Birnin Gwari. Ya kasance Jami’i mafi hazaka a wani darasi na musamman na NAF da aka yi kwanan nan a Bauchi.

“Mun rasa hazikan jami’ai da dama ga rashin tsaro da ya addabi kasarmu. Ya zama dole jami’an gwamnati da yan siyasa su fuskanci wannan matsala.

"Ya zama dole su karkatar da makudan kudaden da ake lalatawa wajen almubazaranci zuwa ga wannan matsala sannan a tabbatar da kashe ko wani kwabo a bayyane.”

A wani labarin kuma, wani sojan Najeriya mai suna Emmanuel, a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba, ya nuna alhini a kan mutuwar wasu abokan aikinsa da suka mutu a filin daga.

Emmanuel ya wallafa hotunan abokan nasa wadanda ya ce sun mutu a yayin arangama da ‘yan ta’addan Boko Haram a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno, shafin Linda Ikeji ta ruwaito.

Ku tuna cewa akalla sojoji ashirin aka kashe sannan wasu da dama suka bata bayan hare-hare mabanbanta da kungiyar ISWAP wacce ta balle daga Boko Haram suka kai Borno a makon da ya gabata.

A cewar Emmanuel, sojojin sun “mutu a filin daga yayin arangama da mayakan Boko Haram a Maiduguri.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel