Kungiyar Dillalan mai, DAPPMAN, sun yi maraba da daina biyan tallafin mai

Kungiyar Dillalan mai, DAPPMAN, sun yi maraba da daina biyan tallafin mai

Kungiyar DAPPMAN ta manyan dillalan kayan mai sun yabawa matakin gwamnatin tarayya na kyale kasuwa ta tsaida farashin sarin man fetur.

A wani jawabi da shugaban DAPPMAN na kasa, Winifred Akpani, ya fitar, ya yabi aikin shugaban kasa Muhammadu Buhari, tare da ba shi shawara.

Winifred Akpani ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki mataki na gaba wajen ganin ta cire hannunta gaba daya daga shiga sha’anin harkar mai.

Shugaban wannan kungiya ya na so gwamnati ta kyale ‘yan kasuwa su ci karensu babu babbaka wajen tsaida farashin fetur domin bunkasa tattalin kasa.

A watan Maris aka shigo da sabon tsari inda ake tsaida farashin litar man fetur bayan an yi la’akari da abin da aka kashe da farashin danyen mai.

Mista Akpani ya ce DAPPMAN ta na maraba da wannan mataki da aka dauka, kuma su na masu ba gwamnati cikakken goyon baya a kan wannan tsari.

KU KARANTA: Buhari ya yi daidai da ya cire tallafin mai inji Sanusi II

Kungiyar Dillalan mai, DAPPMAN, sun yi maraba da daina biyan tallafin mai
Mai ya koma N160 bayan zare tallafi
Asali: Facebook

A cewar kungiyar, tsaida farashi da tallafi da gwamnati ta daina yi zai taimaka wajen kawo gaskiya da takara tsakanin ‘yan kasuwa, tare da inganta tattalin arziki.

“DAPPMAN ta na sane da maganganun da ake yi game da kiran gwamnati ta cire hannunta a ‘yan shekarun nan, kuma mun yarda su na da muhimmanci.” Inji Akpani.

“Sai dai mun yi imani cewa za a shawo kan wadannan matsaloli nan gaba idan gwamnati ta cire hannunta daga harkar mai, ta batar da wannan kudi wajen kawo cigaban kasa, samar da aikin yi, kawo sauyi a harkar noma, da sha’anin ilmi da kiwon lafiya.”

Bayan duk wadannan tarin amfani da za a gani a wasu bangarori, DAPPMAN ta ce cire tallafin mai zai sa gwamnati ta taimakawa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa.

Kamfanonin da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya za su amfana da wannan tsari, haka zalika kasar za ta samu ‘yan kasuwa da su shigo, su zuba jari.

Idan za ku lura, ra’ayin Akpani ya zo daidai da na tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel