'Duk lauya Musulmi da ya ce zai kare wanda ya zagi Annabi Muhammadu (SAW) ya kafurta' - Malami

'Duk lauya Musulmi da ya ce zai kare wanda ya zagi Annabi Muhammadu (SAW) ya kafurta' - Malami

- Shugaban kungiyar Malaman Izala na jihar Sokoto, Sheikh Abubakar Usman Mabera ya yi sharhi kan kare mawakin jihar Kano, Yahaya Aminu Sharif a kotu

- Mabera ya ce duk lauyan da ya kare mawakin wanda kotun Musulunci ta yanke wa hukuncin kisa kwanan nan toh ya kafurta

- Malamin wanda ya kasance babban limamin masallacin Malam Buhari Dan Shehu a Sokoto ya yi kira ga lauyoyi Musulmai da su kiyayi kare mai laifin

Shugaban kungiyar Malaman Izala na jihar Sokoto, Sheikh Abubakar Usman Mabera ya ce duk wani lauya da ya kare mawakin jihar Kano, Yahaya Aminu Sharif wanda kotun Musulunci ta yanke wa hukuncin kisa kwanan nan toh ya kafurta.

Da yake magana a Sokoto a karshen mako, Shehin Malamin ya tabbatar da cewar kotun shari’a da ta isa a Kano ta yanke wa mawakin hukuncin kisa saboda batanci ga Annabi.

Ya bayyana cewa yin batanci ga Annabi a addinin Musulunci ya tanadi hukuncin kisa, cewa “a matsayinsa na Musulmi, wannan hukunci ya hau kan mawakin."

Malamin wanda ya kasance babban limamin masallacin Malam Buhari Dan Shehu a Sokoto ya yi kira ga lauyoyi Musulmai da su kiyayi kare mai laifin.

Ya ce lallai duk lauyan da ya fito domin kare shi toh ya sanar da fitarsa daga addinin Musulunci.

'Duk lauya Musulmi da ya ce zai kare wanda ya zagi Annabi Muhammadu (SAW) ya kafurta' - Malami
'Duk lauya Musulmi da ya ce zai kare wanda ya zagi Annabi Muhammadu (SAW) ya kafurta' - Malami
Asali: UGC

A cewarsa tunda kotun shari’a da ta isa a Kano ta gabatar da hujjar cewa Sharif ya zagi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, toh babu wata mafita sama da hukuncin da Allah ya zartar.

Malamin Musuluncin ya kuma yi kira ga mutane da su koma ga mahaliccinsu sannan su nemi yafiyarsa, cewa dukkanin wadannan annoba da ke sauka a kasar alamu ne na sabo.

KU KARANTA KUMA: Mun kashe N31 biliyan cikin watanni 4 don yaki da korona – Gwamnatin tarayya

Ga dukkan alamu, Allah na fushi damu kuma ya zama dole mu tuba saboda Shi kadai ne maganin bakin cikinmu, in ji shi.

Ku tuna, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ce idan lokacin da aka dibar wa mai laifin ya kai kuma bai daukaka kara ba, toh zai rattaba hannu a kan hukuncin kisan. Tuni dai Sharif ya daukaka kara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel