Za mu binne Oshiomhole ta fuskacin siyasa, in ji Obaseki
- Gwamna Godwin Obaseki ya ce zai binne Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a siyasance a zabe mai zuwa
- Obaseki wanda ya kasance dan takarar PDP ya ce zaben ranar 19 ya watan Satumba zai kasance takara da Oshiomhole
- Gwamnan na Edo ya zargi Oshiomhole da rashin mutunta al'umman jihar
Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo, ya ce zai binne Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a siyasance a zabe mai zuwa.
Da yake magana a lokacin kamfen din jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Oredo da ke jihar a ranar Asabar, Obaseki ya ce zaben ranar 19 ya watan Satumba zai kasance takara da Oshiomhole.
Gwamnan wanda ya kasance dan takarar PDP a zaben, ya ce Oshiomhole, wanda ya sauka daga kujerar shugabancin jihar kafin ya hau, zai dandana kudarsa a zaben saboda baya ganin mutuncin mutanen jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.
“A matsayina na gwamna mai ci, Oshiomhole ya yanke hukuncin daukar wanda zai wakilceni a majalisa ta. Wani irin cin mutunci ne wannan? Daga nan ne yakin ya fara,” in ji gwamnan.
“Saboda ya yarda a zuciyarsa cewa mutanen Benin tamkar kaji suke. Idan k watsa masu masara, Za su bi wannan masarar.
KU KARANTA KUMA: Maigadi ya rasu bayan ya sha giya sannan ya kwanta da takunkumin fuska
“Wannan zaben takara ne da Oshiomhole. Mun gasa masa aya a matakin kasa, za mu binne shi ta fuskacin siyasa a wannan zaben; saboda ba ya mutunta mutanen Benin, ba ya mutuntamu a Oredo, kuma za mu nuna masa cewa shi ba komai bane.”
Oshiomhole na goyon bayan Osagie Ize-Iyamu, dan takarar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
A gefe guda, manyan yan takara biyu a zaben, Gwamna Godwin Obaseki da Fasto Ize-Iyamu sun rungumi junansu a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, gabannin zabe.
Wannan ci gaban ya wakana ne a fadar Sarkin Benin, Ewuare II a ranar Laraba, Channels TV ta ruwaito.
Hakan ya sa mutane da dama hasashen samun zaman lafiya da kuma kore tashin hankali da ake tunanin zai afku tsakanin manyan jam’iyyun biyu.
Manyan jam'iyyun da ke neman kujerar gwamnan Edo dai sune Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) a Edo.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng