Karin kudin wutar lantarki da man fetur ya jawo zanga-zanga a Jihar Osun

Karin kudin wutar lantarki da man fetur ya jawo zanga-zanga a Jihar Osun

- An samu wadanda su ka fita su na zanga-zangar lumana yau a Garin Osogbo

- Mutane su na nuna rashin goyon bayan karin farashin mai da wuta da aka yi

- Wannan ne karon farko da aka samu labarin zanga-zanga a kan karin farashin

Wasu ‘ya ‘yan kungiyoyi masu zaman kansu a jihar Osun sun gabatar da zanga-zanga domin nuna rashin jin dadin karin farashin kudin wuta da man fetur.

A ranar Juma’a, 4 ga watan Satumba, 2020, aka wayi gari a babban birnin Osogbo na jihar Osun da zanga-zanga dalilin karin da gwamnatin tarayya ta yi.

A cikin makon nan ne aka kara farashin shan wutan lantarki, bayan haka farashin litar man fetur ya kara kudi zuwa har fiye da N160 a wasu gidajen mai a kasar.

Jaridar Punch ta ce masu nuna rashin goyon bayan wannan mataki da gwamnati ta dauko sun faro zanga-zangar lumanarsu ne daga Freedom Park a Osogbo.

Rahoton ya bayyana cewa an fara wannan zanga-zanga ne da kimanin karfe 8:30 na safen yau.

KU KARANTA: Tsadar abinci: ‘Yan Najeriya sun yi kaca-kaca da Shugaba Buhari

Masu zanga-zangar su na dauke da alamun da ke nuna fushinsu karara a kan karin kudin wutan lantarki da kuma kudin man fetur.

Wasu daga cikin masu wannan zanga-zanga sun koka da cewa karin kudin wuta da mai da aka yi, ya fito da rashin tausayin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnatin tarayya ta bakin karamin ministan harkokin man fetur, ta ce wannan kari da aka samu a farashin litar man fetur ya fi karfin shugaban kasa.

Zuwa lokacin da mu ka samu wannan rahoto, ana gabatar da zanga-zangar cikin kwanciyar hankali ba tare da an samu wani tashin hankali ba.

Dazu kun ji cewa gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya kare gwamnatinsu ta APC, ya ce ya zama dole fetur ya kara kudi tun da danyen mai ya dada daraja a kasuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel