Zance ya kare: Mahaifin Messi ya yanke hukunci akan abinda yake so dan shi yayi

Zance ya kare: Mahaifin Messi ya yanke hukunci akan abinda yake so dan shi yayi

- Mahaifin Lionel Messi ya amince da dan nashi ya cigaba da zama a kulob din Barcelona

- Jorge ya ce yana so Messi ya kammala kwantiraginsa da kulob din ya tafi salin alin

- Messi dai ana sa ran da zai koma kulob din Manchester City ne na Ingila.

Jorge wanda yake mahaifi a wajen fitaccen dan wasan kwallon kafa Lionel Messi ya bayyana cewa tauraron dan nashi zai cigaba da zama a Barcelona har zuwa karshen kwantiraginsa na 2020/21.

Wannan shawara da ya yanke za ta zama babban cigaba ga kulob din na Barcelona da kuma masoyan kulob din, duba da yadda hankalinsu ya tashi lokacin da ya bayyana kudurinsa na barin kulob din.

Lionel Messi ya bayyana hakane bayan kulob din ya sha kaye a hannun kulob din Bayern Munich a wasan zakarun Turai da ci 8-2, inda hakan ya kawo karshen wasan su a wannan zango.

Zance ya kare: Mahaifin Messi ya yanke hukunci akan abinda yake so dan shi yayi
Zance ya kare: Mahaifin Messi ya yanke hukunci akan abinda yake so dan shi yayi
Source: Facebook

Wannan kaye da suka sha a hannun Bayern Munich shine babban abin kunya da kulob din na Barcelona yayi a tarihi, hakan ya sanya rikici ya nemi ballewa a kulob din.

Manajan kulob din Setien, an kore shi daga kulob din bayan shugabannin kulob din sun nuna bacin ransu kan wannan sakamako na wasa da Bayern Munich, inda suka dauko Ronald Koeman ya maye gurbin shi.

KU KARANTA: Yana da 'yancin da zai yi abinda ya ga dama da rayuwar shi - Sergio Ramos ya goyi bayan Messi

A rahoton da wata majiya ta ruwaito, mahaifin Messi ya bayyana cewa ganawar da yayi da shugabannin na Barcelona komai ya tafi yadda ya kamata.

Da aka tambayeshi idan dan wasan zai zauna a kulob din har zuwa karshen kwantiraginsa a shekarar 2021, Jorge ya bada amsa da 'eh'.

Idan ba a manta ba Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda dan wasan kulob din Real Madrid Sergio Ramos ya bayyana cewa Messi ya cancanci a bashi damar da zai tsara rayuwarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel