Dapo Abidoun ya na goyon bayan karin kudin wuta da maida litar fetur N162

Dapo Abidoun ya na goyon bayan karin kudin wuta da maida litar fetur N162

- Dapo Abiodun ya ce jama’a za su iya sayen litar man fetur a kan N160

- Abiodun ya nuna goyon baya game da karin da gwamnatin APC ta yi

- Gwamnan ya ce tun da an sha mai da araha, dole yanzu a saya da tsada

A daidai lokacin da Bayin Allah su ke cigaba da kokawa game da karin kudin wutan lantarki da man fetur da aka yi, gwamnan jihar Ogun, ya yi magana.

A jiya Alhamis, Dapo Abiodun ya nuna goyon bayansa a kaikaice a kan karin kudin shan wutar lantarki da kudin litar man fetur da gwamnatin Najeriya ta yi.

Gwamnati ta maida farashin saida mai a manyan tashoshi N150 zuwa N152, wanda hakan ya sa ake saida litar man fetur a kan kusan N160 a gidajen mai.

Gwamna Abiodun ya hadu da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 3 ga watan Satumba, 2020, inda ya zanta da ‘yan jarida bayan haduwarsu.

Dapo Abiodun ya ziyarci fadar shugaban kasar ne domin ya gabatarwa Buhari wata takarda da ke dauke da jerin ayyukan da ya yi a shekarar farko a kan mulki.

KU KARANTA: ‘Yan kasuwa sun gargadi ‘Yan Najeriya su kara shiryawa karin kudin fetur

Dapo Abidoun ya na goyon bayan karin kudin wuta da maida litar fetur N162
Abidoun ya ce kasuwa ta canza shiyasa fetur ya tashi
Source: Twitter

Jaridar The Guardian ta rahoto Abiodun ya na cewa mutane za su iya jurewa sabon karin farashin mai da aka yi domin a baya sun kasance ba su biyan kudi mai yawa

Gwamnan ya zargi al’umma da son cin banza, ya ce mutane su na son ganin sun saye mai da araha a lokacin da ya karye, sannan ba su son kashe kudi idan ya yi tsada.

“Na farko dai ku na so ku more farashi mai araha a lokacin da darajar danyen mai ya yi kasa, sannan ba ku son ku biya karin kudi lokacin da farashin danyen mai ya canza.”

“Farashin danyen mai ya na zama kai-da-kai ne da kudin tataccen mai.” Inji Abiodun.

Yayin da gwamnan mai shekara 60 ya ke wannan magana, kungiyar kwadago ta reshen jiharsa sun bashi wa’adin biyan kudin ma’aikata ko su tattara su tafi yajin aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel