Zaben cike gurbi: Sabon rikici ya kunno kai a APC yayinda fusatattun ‘ya’yanta suka yi zanga-zanga

Zaben cike gurbi: Sabon rikici ya kunno kai a APC yayinda fusatattun ‘ya’yanta suka yi zanga-zanga

- APC reshen Bayelsa na fuskantar sabon rikici kasa da watanni biyu kafin zaben cike gurbin sanatoci

- Fusatattun shugabannin jam’iyyar sun aika korafi zuwa ga shugaban kwamitin rikon kwarya kan gudanarwar shugaban jihar

- Mambobin APC na zargin Timipre Sylva da shirin tursasa masu ‘yan takara ba tare da tuntuba ba

Sabon rikici na kunno kai a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Bayelsa kasa da watanni biyu kafin zaben cike gurbi na sanatoci a jihar.

Wasu fusatattun shugabannin jam’iyyar daga yankunan Bayelsa ta tsakiya da Bayelsa ta yamma sun abatar da korafi ta hannun lauyansu, Rueben Egwaba kan gudanarwar Timipre Sylva jigo ga shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar a jihar.

Fusatattun mambobin jam’iyyar APC a wasikar sun yi kira ga Shugaban kwamitin rikon kwaryan da ya dakatar da Sylva da sauransu daga tursasa masu yan takara domin kawar da annobar da ke shirin samar jam’iyyar.

Zaben cike gurbi: Sabon rikici ya kunno kai a APC yayinda fusatattun ‘ya’yanta suka yi zanga-zanga
Zaben cike gurbi: Sabon rikici ya kunno kai a APC yayinda fusatattun ‘ya’yanta suka yi zanga-zanga Hoto: The Guardian
Source: Twitter

An tattaro cewa shugabannin jam’iyyar sun yi zargin cewa Sylva na aiki domin tursasa masu yan takara wadanda suka sauya shekar daga jam’iyyar People’s Democratic Party.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo 2020: Obaseki da Ize Iyamu sun kulla yarjejeniya gaban Sarkin Benin

Har ila yau sun ce wadannan mutane basu kai adadin ranakun da zai sa su cancanci neman mukaman siyasa ba.

Sun yi gargadin cewa yunkurin tursasa wadannan mutane zai haifar da matsala.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa zabar yan takara na zaben cike gurbin yan majalisar dokokin tarayyar a jihar Bayelsa ya tarwatsa PDP a jihar mai albarkatun mai.

Wasu daga cikin fusatattun magoya bayan jam’iyyar a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, sun yi zanga-zanga.

Sun yi hakan ne kan zargin hana tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Monday Obolo, da wasu biyu yin takarar kujerar cike gurbi na majalisar dokokin ba bisa ka’ida ba.

Sauran wadanda aka hana takarar sune tsohon sakataren gwamnatin jihar Bayelsa, Gideon Ekowe da tsohon darakta janar na hukumar BGIS, Igo Assembly Goin.

An tattaro cewa kwamitin tantancewa na jam’iyyar PDP ta hana yan takarar uku tsayawa saboda takarar tsohon Shugaban jam’iyyar PDP, Cleopas Moses.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel