Ba-ta-kashi: Yadda haduwar sojoji da 'yan bindiga ta kasance a Kaduna

Ba-ta-kashi: Yadda haduwar sojoji da 'yan bindiga ta kasance a Kaduna

Rundunar Operation Accord sun kashe wasu ‘yan bindiga hudu a yankin Jeka Da Rabi da ke hanyar babbar titin Kaduna-Abuja a jihar Kaduna sannan sun samo makamai daga hannunsu.

Shugaban sashin labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne ya tabbatar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Alhamis.

An tattaro cewa aikin wanda ya gudana a ranar 2 ga watan Satumba, ya kasance ci gaban mummunan yaki da ake a kan ‘yan bindiga da sauran miyagu a kasar.

“Da suke aiki kan bayanan kwararu kan shige da ficen ‘yan bindiga daga yankin Kachia, an tura dakaru zuwa yankin sannan sun kaddamar da harin bazata.

“Dakarun sojojin sun hadu da yan bindigan sannan suka yi arangama da su, suka kuma bude masu wuta wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum hudu sannan sauran sun tsere da raunukan bindigohi,” in ji sanarwar.

Kakakin rundunar tsaron ya ce sojojin sun kuma samo wani bindigar AK 47 da alburusai 5 tare da wani mujalla sannan sun mamaye yankin gaba daya da fatirol ba kakkautawa a kokarinsu na neman ‘yan bindigar da suka tsere.

Da take martani kan lamarin, babbar hukumar sojin ta bukaci dakarun da su jajirce a yakin da suke kan miyagu a kasar.

Yan kwanakin nan, Kaduna ta fuskanci hare-haren yan bindiga daban-daban wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama da dukiyoyi.

Biyo bayan mummunan lamarin, rundunar sojin sama a ranar 16 ga watan Agusta ta tura sabbin runduna na musamman zuwa kudancin Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo 2020: Obaseki da Ize Iyamu sun kulla yarjejeniya gaban Sarkin Benin

Aika rundunar da aka yi ya haifar da ‘ya’ya masu idanu yayinda aka kama wasu yan bindiga sannan aka kashe wasu da dama lokacin aikin sojoji.

Kimanin makonni biyu da suka gabata, sojojin sama sun yi barin wuta ta sama, sun kashe yan bindiga da dama a sansaninsu da ke dajin Kuduru na jihar.

A cewar hukumar sojin, an lalata sansanin yan bindiga na mambobin Ansaru karkashin jagorancin wani Mallam Abba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel