Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda farashin abubuwa su ke kara tsada

Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda farashin abubuwa su ke kara tsada

Ganin yadda abubuwa su ke kara wahala a Najeriya, mutane da-dama su na cigaba da tofa albarkacinsu game da sha’anin tattalin arzikin kasa.

Wani daga cikin fitattun wadanda su ka yi magana shi ne Sanata Shehu Sani, wanda ya taba wakiltar yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa.

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa farashin komai ya na tashi ne a gwamnatin APC, ya nuna cewa babu abin da kudinsa ya ke yin kasa a halin yanzu.

A cewar babban ‘dan siyasar, bashin kudin kasar waje da ake bin Najeriya ya karu, haka zalika kudin shan wutan lantarki da kuma farashin litar man fetur.

Alkaluma sun nuna babu shakka gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta karbo bashin kudi daga kasashen waje masu matukar yawa a shekaru biyar.

A jiya Laraba, 2 ga watan Satumba ne kuma aka ji labarin karin farashin kudin man fetur. Kafin nan an bada sanarwar samun sauyi a farashin lantarki a ranar Talata.

KU KARANTA: Ana korafi a kan karin kudin wuta da farashin man fetur

Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda farashin kaya ke kara tsada a Najeriya
Shehu Sani ba ya goyon bayan karin kudin wuta
Source: Twitter

Sani ya ce har kudin ‘data’ da ake amfani da shi wajen ziyarar yanar gizo ya kara kudi. Sai dai gwamnati ta na kokarin ganin kamfanoni sun rage farashinsu.

Sanatan ya kara da cewa kudin buhun shinkafa da harajin kayan masarufi sun karu a kasar.

Babu shakka yanzu kudin buhun shinkafar gida ta kai N23, 000, kudin shinkafar gwamnati kuwa ta zarce hakan. A shekarar nan kuma an kara harajin VAT.

Tsohon ‘dan majalisar tarayyar ya ce duk da wadannan, ana fuskantar tsadar rayuwa da kudin makarantar boko, a cewarsa duk kudinsu ya tashi sama.

A cewarsa abubuwan da darajarsu ta yi kasa su ne farashin Naira da kuma asusun kudin kasar waje. A makon jiya an saida Dalar Amurka a kan N470.

A watannin baya an samu rahoton cewa akwai fam Dala biliyan 36.5 a cikin asusun kudin kasar wajen Najeriya, fiye da abin da ake da shi a shekarar 2019.

Mun kuma ji Shehu Sani ya yi kira ga mutane su nuna rashin goyon baya ga karin kudin lantarki, yayi duk wadannan jawabai ne a shafinsa na Twitter jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel