Zaben Edo 2020: Obaseki da Ize Iyamu sun kulla yarjejeniya gaban Sarkin Benin

Zaben Edo 2020: Obaseki da Ize Iyamu sun kulla yarjejeniya gaban Sarkin Benin

- A karshe, Gwamna Godwin Obaseki da Fasto Osagie Ize-Iyamu sun amince da zaman lafiya gabannin zaben gwamnan Edo

- Harma ta kai yan takarar biyu na APC da PDP sun rungumi junansu a fadar Oba Ewuare II

- Hakan ya karfafa muradin cewa za a yi zabe mai zuwa cikin lumana

A kokarin ganin an wanzar da zaman lafiya da gaskiya gabannin zaben gwamnan Edo, manyan yan takara biyu, Gwamna Godwin Obaseki da Fasto Ize-Iyamu sun rungumi junansu a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba.

Wannan ci gaban ya wakana ne a fadar Sarkin Benin, Ewuare II a ranar Laraba, Channels TV ta ruwaito.

Hakan ya sa mutane da dama hasashen samun zaman lafiya da kuma kore tashin hankali da ake tunanin zai afku tsakanin manyan jam’iyyun biyu.

Manyan jam'iyyun da ke neman kujerar gwamnan Edo dai sune Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) a Edo.

Zaben Edo 2020: Obaseki da Ize Iyamu sun kulla yarjejeniya gaban Sarkin Benin
Zaben Edo 2020: Obaseki da Ize Iyamu sun kulla yarjejeniya gaban Sarkin Benin Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Cikin manyan yan siyasa da masu ruwa da tsaki da suka halarci taron zaman lafiyar a fadar sarkin harda Adams Oshiomhole, John Oyegun, da mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.

Da yake jawabi a kan alamun rikici gabannin zaben, Sarkin ya yi kira ga dukkanin mambobi a jihar da su rungumi zaben lumana.

Sarkin ya kuma tunatar dasu cewa dukkansu yan uwan juna ne.

KU KARANTA KUMA: Haduwar Ganduje da Osinbajo a Abuja: An bayyana batutuwan da suka tattauna akai

Oba Ewuare ya ce: “A wajena, su (yan siyasa a Edo) duk yan uwan juna ne, kuma menene ba za a iya magancewa ba idan kuka kasance yan uwa?

“Yan uwa na iya fada amma dole su sasanta. Yau, wannan shine abunda nake so mu cimma; dole akwai maslaha.”

A wani labari na daban, am'iyyar APC, ta soke taron yaƙin neman zaɓe da ta shirya yi bayan hadarin mota da ya ritsa da magoya bayan ta da wasu ƴan sanda.

An shirya ƴin taron yaƙin neman zaben ne da nufin janyo hankalin masu zabe a garin ta Usen su zabi jam'iyyar ta APC.

Mai magana da yawun kwamitin kamfen din APC, John Maiyaƙi, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce trela ce ta bi ta kan wasu motoci a tawagar jiga-jigan jam'iyyar.

Ciki har da tsohon shugaban jam'iyyar na ƙasa, Adams Oshiomhole kafin Ojukwu junction a Benin City, babban birnin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng