MURIC: Kiristoci aka cika a jerin wadanda Gwamnati za ta dauki nauyin karatunsu

MURIC: Kiristoci aka cika a jerin wadanda Gwamnati za ta dauki nauyin karatunsu

Kungiyar MURIC mai kokarin kare addinin musulunci ta yi magana game da wadanda gwamnati ta zaba domin su yi karatu a kasashen ketare.

Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar da jawabi, ya ce jerin sunayen da aka fitar na wadanda su ka dace da tsarin BEA na bana ya nuna an zalunci Arewa.

Rahotanni da ke yawo sun nuna cewa mutanen Arewa 21 kacal aka zaba a cikin wadanda za a tura karatu zuwa kasar waje, Kudu kuwa su na da mutane har 70.

Kamar yadda MURIC ta fitar da jawabi, musulmai 13 rak aka zaba daga yankin Arewa maso tsakiya, ta ce wannan ya nuna shirin kiristantar da bangaren kasar.

Farfesa Ishaq Akintola ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta fito ta kare kanta, ta nunawa Najeriya cewa babu makarkashiyar danne addinin musulunci da musulmai.

Daily Nigerian ta rahoto Farfesan ya na cewa shirin ya nuna kiyayya ga addinin musulunci, a cewarsa da wannan sun gano boyayyen shiri na kiristantar da kasar.

KU KARANTA: Gwamnatin China ta hana amfani da sunaye irinsu Muhammad

MURIC: Kiristoci aka cika a jerin wadanda Gwamnati za ta dauki nauyin karatunsu
Shugaban kungiyar MURIC, Ishaq Akintola
Asali: UGC

“Ko da mu na zaton jerin sunayen da aka fitar labarin bogi ne kuma aikin abokan gaba, amma duk da haka dole gwamnatin tarayya ta fito ta yi magana kafin a samu matsala.”

Wannan kungiya ta MURIC ta ce yanzu haka ana fama da rashin yarda tsakanin mutanen yankin kudu da arewa da kuma bangaren musulmai da kiristoci a fadin Najeriya.

“Ana amfani da wannan wajen jefa harkar addini cikin siyasa, musamman ana fifita daukar tsirarun musulmai a yankin da musulmai su ke da rinjaye.” Inji Akintola.

Sai dai kamar yadda MURIC ta ke zargi, wannan sunaye da aka fitar na bogi ne. Gwamnatin tarayya ta ce jerin da ake gani ya na yawo a gari, sam ba na gaskiya ba ne.

“Ba za mu amince da nunawa wata kabila bambanci ba. Za mu cigaba da tsayawa gaskiya da adalci. Zaman lafiya da cigaba shi ne babban abin da ke gaban MURIC.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel