Abin da kwamitin Buni ya ke shirin yi a Zamfara, wasa da hankalin kotu ne inji Bakyasuwa

Abin da kwamitin Buni ya ke shirin yi a Zamfara, wasa da hankalin kotu ne inji Bakyasuwa

Bangaren jam’iyyar APC da ke tare da Sanata Kabir Garba Marafa a jihar Zamfara ta yi wa kwamitin rikon kwarya na Malam Mai Mala Buni raddi.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a Zamfara, Alhaji Bello Bakyasuwa, ya yi magana game da sabon umarnin da aka bada na ruguza barin Sirajo Garba.

Bello Bakyasuwa ya yi hira da ‘yan jarida a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, ya ce yunkurin fifita bangaren Abdullaziz Yari a kansu, ya sabawa kotu.

Jigon jam’iyyar da ake yi wa kallon ‘yan tawaye ya ce kotu ta riga ta bada umarni a ruguza duk wasu bangarorin jam’iyyar APC a Zamfara, a shirya sabon zabe.

Bakyasuwa ya ke cewa: “Ba ku da labarin hukuncin da kotu ta yi na sauke duk wasu bangarori, da bada umarnin a gudanar da sababbin zabubbuka?”

Shin yin hakan ba zai zama wasa da kotu ba? Alhaji Bakyasuwa ya ke tambaya.

KU KARANTA: Zamfara: Kwamitin Mai Mala Buni-ya ba Marafa rashin gaskiya

Abin da kwamitin Buni ya ke shirin yi a Zamfara, wasa da hankalin kotu ne inji Bakyasuwa
Buni ya bukaci a rusa barin Sirajo Garba a Zamfara
Source: UGC

“Ko da ya ke babu wanda ya tuntubemu; mun dai gani ne a takarda kamar yadda ku ka gani a kafafen sada zumunta na zamani. Za mu yi magana idan aka tuntubemu.

Da aka tambayi sakataren yada labaran na APC ko mutanensa sun janye karar da su ka kai jam’iyya kamar yadda NEC ta bukata, sai ya ce babu wannan maganar.

“Kamar yadda wane ya bada umarni? A yaushe? Ba mu taba yin wannan maganar ba da uwar jam’iyya ko a madadin shugabannin rikon kwarya ko wani.” Inji sa.

Alhaji Bakyasuwa ya nuna ya na shakkar jam'iyyar APC a karkashin shugaba Muhammadu Buhari za ta yi watsi da umarnin kotu, ko ta sa a hukuntasu.

“Ina zaton an kafa kwamitin rikon kwarya ne domin shawo kan matsalolin APC, ba don a kara jagwalgwala lamarin ba. Ba ka shawo kan matsala ta hanyar daukar bangare.”

Yaran na Kabir Marafa su ka ce ya kamata shugabannin rikon APC su yi masu adalci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel