Kulob din Barcelona ya bayyana abinda zai yiwa Messi matukar ya bar kulob din

Kulob din Barcelona ya bayyana abinda zai yiwa Messi matukar ya bar kulob din

- Kokarin da Lionel Messi yake yi na barin kulob din Barcelona zai iya karewa a kotu

- Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan na kasar Argentina yana shirin kammala yarjejeniya da kulob din Manchester City na Ingila

- Lamarin dai yayi kamari, yayin da Barcelona take shirin kai shi kotu

Kokarin da Messi yake yi na barin Barcelona ya canja salo yayin da kulob din yayi barazanar cewa matukar dan wasan ya kammala yarjejeniya da Manchester City to duka za su bayyana a gaban kotu.

Lamarin dai a kasar Spain yayi kamari yayin da kulob din ya bayyana cewa za ta kai duk kulob din da ya dauki dan wasan.

Kulob din Barcelona ya bayyana abinda zai yiwa Messi matukar ya bar kulob din
Kulob din Barcelona ya bayyana abinda zai yiwa Messi matukar ya bar kulob din
Source: UGC

Messi dai ya bawa kowa mamaki, yayin da ya bayyana shirinsa na barin kulob din na Barcelona a makon da ya gabata, yayin da yayi kokarin kawo karshen kwantiraginsa, ya kuma nemi kulob din ya bari ya tafi.

KU KARANTA: Yawan kudin da Messi yake dauka a kulob din Barcelona duk shekara

Kulob din ya bayyana cewa kwantiragin dan wasan ya kare tun a watan Yuni, saboda haka dole dan wasan ya biya fam miliyan 629, idan har yana so ya bar kulob din.

Wata majiya daga kasar Birtaniya ta ruwaito cewa dan wasan ya amince zai koma kulob din Manchester City akan kudi Euro miliyan 700, daidai da kudin da ake so ya biya a kulob din Barcelona a matsayin kudin da zai biya kafin su bar shi ya tafi.

Messi ya amince da wannan doka ta kudi da aka sanya masa, inda zai biya a cikin shekara biyar idan kulob din Manchester City sun dauke shi.

An gano cewa Messi zai yi wasa a kulob din Manchester City na tsawon shekara uku daga nan kuma zai koma wani kulob din ya buga na tsawon shekara biyu.

An ruwaito cewa mahaifin Messi Jorge ya isa kulub din Manchester City a ranar Laraba da safe, kuma zai gana da shugabannin kulob din don daidaita matsalar da ake fama da ita kan dan wasan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel