Tsaro: Rundunar 'yan sanda ta nufi sarakunan arewa da kokon bara

Tsaro: Rundunar 'yan sanda ta nufi sarakunan arewa da kokon bara

Babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu, ya roki sarakunan gargajiya su bawa gwamnati goyon baya a kokarinta na ganin bayan fashi da makami, garkuwa da mutane, barnar 'yan bindiga, da satar shanu.

Mista Adamu, wanda kwamishinan 'yan sandan jihar Neja, Adamu Usman, ya wakilta, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da ma su rike da sarautun gargajiya na masarautar Kontagora.

An yi muhimmiyar ganawa a tsakanin rundunar 'yan sanda da ma su rike da sarautar gargajiya a masarautar Kontagora domin tattauna yadda za a samu nasarar tabbatar da tsaro a tsakanin al'umma.

Ma su rike da sarautar gargajiya daga masarautar Kontagora a karkashin jagoranci babban sarkinsu, Saidu Namaske, sun ziyarci hedikwatar 'yan sanda ta jihar Neja da ke birnin Minna domin yi musu godiya.

Sun bayyana cewa sun ziyarci hedikwatar ne domin taya rundunar 'yan sanda murnar samun nasara a yakin da take yi da aikata miyagun laifuka a jihar Neja.

A sakonsa, IGP Adamu ya ce rundunar 'yan sanda za ta cigaba da hada kai da masu ruwa da tsaki domin magance kalubalen tsaro a jihar Neja.

Ya bukaci a sanar da rundunar 'yan sanda motsin duk wasu masu laifi ko 'yan ta'adda domin gaggauta daukan mataki a kansu.

IGP ya bayyana cewa an kara yawan jami'an 'yan sanda zuwa karkara da kauyuka domin su zakulo duk wasu wurare da 'yan bindiga da 'yan ta'adda ke fakewa da tafka barna.

A nasa jawabin, mai martaba Namaske ya ce mutanen masarautar Kontagora suna mika godiyarsu ga rundunar 'yan sanda a kan daukan matakan da suka rage matsalolin fashi da makami, garkuwa da mutane, da satar shanu.

"Yanzu mazauna Rijau, Magana, Wushihi, Kontagora, Mashegu da karamar hukumar Mariga sun cigaba da gudanar da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba.

"Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta dawo mana da zaman lafiya ta hanyar kafa sashe na musamman domin inganta tsaro a tsakanin jama'a.

"An kafa sansanin 'yan sanda a karkara, mun yi mtukar farin ciki da hakan, saboda tsaro ya inganta," a cewarsa.

Babban basaraken ya bukaci sauran hukumomin tsaro su cigaba da kokarin da suke yi na tabbatar da samun zaman lafiya jihar Neja da sauran sassan Najeriya.

Kazalika, ya bayar da tabbacin cewa zasu cigaba da bawa hukumomin tsaro gudunmawa ta kowanne bangare domin samar da tsaro.

"Za mu cigaba da bawa rundunar 'yan sanda muhimman bayanai da zasu kai ga kama duk wasu batagari a cikin al'umma. Wannan nauyi ne da ya rataya a wuyanmu, wanda kuma ba zamu yi wasa da shi ba," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel