Ya kamata yanzu litar man fetur ta koma N155 Inji Adetunji Oyebanji

Ya kamata yanzu litar man fetur ta koma N155 Inji Adetunji Oyebanji

Shugaban kungiyar manyan ‘yan kasuwan mai na Najeriya, Adetunji Oyebanji, ya ce ya kamata farashin litar man fetur ya kai kusan N155.

Mista Adetunji Oyebanji wanda shi ne shugaban kamfanin 11 PLC (tsohon kamfanin Mobil Oil Nigeria Plc) ya shaidawa CNBA Africa wannan a jiya.

A watan Agustan da ya wuce ne gwamnati ta yi karin kudi a kan farashin man fetur inda aka koma saida man tsakanin N148 zuwa 150 a fadin Najeriya.

Yanzu an shiga sabon wata amma hukumar PPPRA da ke tsaida farashi a madadin gwamnati ba ta ce komai game da yadda za a saida fetur a gidajen mai ba.

Adetunji Oyebanji ya ce akwai bukatar a sake kara kudin lita a watan nan, a cewarsa man fetur ya kara kudi don haka ya kamata ayi watsi da tsohon farashi.

Oyebanji ya ke cewa NNPC ta biya N5.35b a watan Yuni ne a sakamakon asarar da aka yi a dalilin saida litar man fetur tsakanin 148 zuwa 150 a gidajen mai.

KU KARANTA: BUA zai gina matatar da za ta rika tace ganga 200000 a Aka Ibom

Ya kamata yanzu litar man fetur ta koma N155 Inji Adetunji Oyebanji
Ana zargin an dawo da tallafin man fetur
Source: UGC

“Yanzu idan aka duba, za a ga cewa akwai burbushin tallafin man fetur saboda idan aka yi la’akari da farashin da aka tsaida a watan Agusta, ana bada sarin mai a kan N145, ainihin kudin ya kamata ya kai N155.” Inji Oyebanji.

“Idan aka duba lissafin da PPPRA ta ke yi wajen tsaida farashi, za ku ga ko da kudin kasar waje aka kara, kudin zai tashi ba laifi fiye da abin da ake saidawa a kasuwa.”

Ya ce: “Hakika, abubuwa ba su tafiya wara-wara. Mu na zargin akwai wasu abubuwa a kasa.”

‘Dan kasuwan ya ce za su cigaba da aiki da gwamnati domin warware duhun da aka shiga. “Amma dai tabbas, akwai alamun biyan tallafin man fetur.” inji sa.

Mista Oyebanji ya nemi gwamnati ta dakatar da biyan tallafin man fetur, ta kyale farashin mai ya rika tsaida kan shi a kasuwa, kamar yadda wasu masana su ke kira.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel