Ta hanyar zama a tattauna ne za a ga karshen rigimar Kaduna inji Dr. Gumi

Ta hanyar zama a tattauna ne za a ga karshen rigimar Kaduna inji Dr. Gumi

Malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya tofa albarkacin bakinsa game da rikicin jihar Kaduna.

Shahararren malamin ya bayyana tattaunawa domin sulhu a matsayin hanyar da za a samu zaman lafiya tsakanin mabanbantan al’ummar da ke zaune a Kaduna.

A wani jawabi da ya fitar bayan a wani taro da aka shirya, malamin musuluncin ya ce zama a tattauna shi ne abin da addinin musulunci da kiristanci ya koyar.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce ya zama dole mutane su zauna su tattauna da juna da nufin samun hanyar da za su zauna lafiya tsakaninsu.

Ahmad Abubakar Gumi ya na cikin cibiyar kawo zaman lafiya tsakanin addinai a Kaduna.

Malamin ya ke cewa jahilci da kuma talauci su na cikin abubuwan da su ka jawo garkuwa da mutane da ta’addancin Boko Haram da sauransu a Najeriya.

KU KARANTA: Almajirai 2300 sun amfana da tallafi a Arewa - ACRI

Ta hanyar zama a tattauna ne za a ga karshen rigimar Kaduna inji Dr. Gumi
Dr. Ahmad Abubakar Gumi
Asali: Depositphotos

A cewarsa, ana bukatar a rika kira da wayar da kan mutane game da zaman lafiya domin kawo karshen rashin jituwar da ke tsakanin kirista da musulmai a Kaduna.

Bajimin malamin fikihun ya ce da wannan kira na zaman lafiya ne musulmai da kiristoci musamman na kudancin jihar Kaduna da su ke rikici za su sake da juna.

Rabaren Mathew Man’Oso yayi jawabi a madadin bangaren kirista, faston ya ce litattafan addinai sun yi kira ga mabiya su zama masu hakuri da juna domin a zauna lafiya.

“Ana jin maganar malamin addini fiye da ta kawone shugaba, wannan ya ba shugabannin addinai damar taka rawar ganin kawo zaman lafiya.” Inji Rabaren Man’Oso.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng