Miji ya kashe matarsa da yaransa biyu saboda sun dame shi da surutu

Miji ya kashe matarsa da yaransa biyu saboda sun dame shi da surutu

An kama wani uba bisa zargin kashe matarsa da matasan ‘ya’yansa maza su biyu saboda yana jin ciwon kai sannan kuma ya gaji da ihun su.

An kama James Lee Webb, mai shekaru 57 sannan aka tuhume shi da aikata kisan kai bayan ya kira ‘yan sanda da kansa a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, 2020.

Webb da matarsa, Victoria Ronack Bunton, ya fara jayayya da matarsa da misalin karfe 10:00 na safiyar Litinin bayan ya yi korafin cewa yana jin ciwon kai sannan cewa yaranta masu shekaru 13 da 16, suna ta hayaniya, kamar yadda yake a takardar kotun.

A yayin jayayyar sai Webb ya fito da wani bindigar hannu sannan ya harbi Bunton, kafin ya kashe matasan yaran su biyu.

Webb ya tsaya na tsawon sa’a daya sannan ya kira 911 inda ya tona abunda ya yi, in ji takardar, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Lokacin da ‘yan sanda suka iso sai suka tafi dashi zuwa wajensu. Da aka tambaye shi daga bisani, Webb ya fada ma wani jami’i cewa ya gaji da iyalansa suna masa hayaniya sannan suna fada mashi cewa babu abunda ya same shi.

Miji ya kashe matarsa da yaransa biyu saboda sun dame shi da surutu
Miji ya kashe matarsa da yaransa biyu saboda sun dame shi da surutu Hoto: Linda Ikeji
Source: UGC

A yanzu haka yana tsare a kurkukun Lew Sterrett kotun Majistare na Dallas za ta yanke makomarsa.

Makwabi Chanel Lockhart ya fada ma Fox4: “gani na karshe da nayi mata, tana fitar da kayan abinci daga cikin mota sannan yaranta suna taya ta.

“Ba za ka taba tunanin zai aikata hakan ba. Kuma tana da kirki. Kowa na son ta.

“Ba za ka taba tunanin cewa wata rana zai kira sannan ya ce ya kashe yaransa ba.”

KU KARANTA KUMA: FG za ta kara wa'adin shirin daukar mutane 77400 aiki a Nigeria

Wani makwabci, Justis Johnson, ya bayyana cewa: “na san su tsawon shekaru biyu, suna tafiya tare da mamarsu zuwa shagon siyar da kayan abinci, suna taya ta siyar da kaya, suna shiga motar makaranta.

‘Yarsa, Sylvia ta kara da cewa: “bana magana da su sai. Amma idan na fito waje, suna magana. Basa taba wuce ni. Za su ce, sannu.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel