Gwamnonin arewa sun taya Yahaya Bello murna bayan nasarar da yayi a kotun koli

Gwamnonin arewa sun taya Yahaya Bello murna bayan nasarar da yayi a kotun koli

- Kungiyar gwamnonin arewa ta yi martani a kan hukuncin kotun koli da ta tabbatar da zaben Yahaya Bello

- Gwamnonin sun bayyana nasarar Bello a matsayin tabbatar da muradin mutane na karshe

- Shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau, ya kuma yi kira ga tallafa wa gwamnan jihar Kogi

Gwamnonin Najeriya karkashin kungiyar gwamnonin arewa sun taya Yahaya Bello murna biyo bayan nasarar da yayi a kotun koli a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta.

Legit.ng ta tuna cewa kotun koli ta tabbatar da Bello na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kogi.

Kwamitin babbar kotun na mutum bakwai karkashin jagorancin Shugaban alkalan Najeriya, Justis Ibrahim Tanko, ya yi watsi da karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Musa Wada suka shigar.

A hukuncinta, kotun ta tabbatar da hukuncin kotun zabe da kotun daukaka kara cewa masu karar sun gaza tabbatar da ikirarinsu.

Cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta dawo da Bello kan kujerarsa a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 16 ga watan Nuwamba, 2019 ba bisa ka’ida ba.

Gwamnonin arewa sun taya Yahaya Bello murna bayan nasarar da yayi a kotun koli
Gwamnonin arewa sun taya Yahaya Bello murna bayan nasarar da yayi a kotun koli Hoto: Daily Sun
Asali: Facebook

A wani hukuncin kuma, kotun kolin ta yi watsi da bukatar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da ‘yar takarar, Natasha Akpoti, na neman a soke zaben Gwamna Yahaya Bello.

KU KARANTA KUMA: Zaman lafiya zai kare idan aka fitar da sunayen ƴan kwangilar NDDC - Cairo

A wani jawabi daga Gwamna Simon Bako Lalong, wanda shine Shugaban kungiyar, ya bayyana nasarar Bello a kotun koli a matsayin dawo da muradin mutane.

Lalong ya yi kira ga mutanen jihar Kogi da su tallafa wa gwamnan domin kawo ci gaba da damokradiyya jihar, jaridar The Sun ta ruwaito.

A wani labari na daban, Sanata Orji Uzor Kalu ya yi magana game da siyasar cikin gidan jam’iyyar APC da kuma zaben shugaban kasa da za ayi a shekarar 2023.

Yayin da ake maganar mulki ya koma bangaren kudancin Najeriya a zabe mai zuwa, Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa hakan bai fa zama dole ba.

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu ya ja-kunnen masu kiran a tsaida ‘dan takarar shugaban kasa daga Kudu da cewa babu inda aka rubuta wannan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel