Rikici ya barke a kotu, yayin da miji yace ya fasa sakin matarshi bayan Alkali ya riga ya raba auren
An sha ‘yar dirama a kotun gargajiya na Mapo da ke Ibadan, jihar Oyo a ranar Litinin, lokacin da wani gurgu a kan kekensa, Joel Banimore, ya fada ma shugaban kotun cewa ya fasa sakin matarsa bayan kotun ta saurari rokonsa.
Banimore ya shigar da kara kotu cewa yana so a rushe aurensa na shekaru 15 tsakaninsa da matarsa, Abimbola.
Ya bayyana cewa matar tasa ta cika fitina sannan tana bari ‘yan uwanta na yanke hukunci a gidansa, don haka ya shirya barinta ta koma ga ahlinta.
Mai karan ya fada ma shugaban kotun, Cif Ademola Odunlade, “idan ka tuna na fada maka a shekarar da ta gabata cewa matata na cin amanata. Na kamata tana tarayya da wasu dattawa a cocinmu, amma duk da haka, na jure. Kuma na fada maka cewa bata da lafiya ka umurceni da na kula da ita.
“Na dauke ta na kaita UCH, Ibadan, inda aka bukaci na biya N300,000 na magani. Na fada ma yan uwanta bazan iya biya ba sannan na nemi yardarsu domin mu yi amfani da likitan dake duba ahlina, wanda ya nemi mu biya N20,000. Basu amince dani ba. Suka dauke ta suka kaita wajen likitan kawunta, wanda ya chaje su N15,000.
“Na biya kudin, amma hankalina bai kwanta ba. Yan uwanta ne ke yanke wa iyalaina hukunci a koda yaushe. Idan bata shirya saurarona ba, tana iya bin yan uwanta.”
Abimbola ta mayar da martani cewa mijinta “fitinanne ne kuma a koda yaushe yana tayar da rigima, ko ba tare da dalili ba.”
KU KARANTA KUMA: Matsalar tsaro a Arewa: Ka nemi shawarar shuwagabannin Arewa - Sani ya shawarci Buhari
Cif Odunlade ya rushe auren sannan ya umurci Banimore da ya dunga biyan N15,000 duk wata a matsayin kudin abincin yaransu uku, yayinda ya ba wacce ake kara ragamar rike yaran.
Cike da al’ajabin karar da mai korafi ya daukaka bayan yanke hukunci cewa baya so kotu ta raba aurensa da matarsa kuma, Odunlade ya fada masa cewa da ya sani ya yi tunani da kyau kafin ya kai matarsa kotu, ko kuma ma ya janye karar kafin zartar da hukunci.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng