Zaben 2020: PDP ta yi kira ga mutane su fita su yi zaben Gwamna a Jihar Edo

Zaben 2020: PDP ta yi kira ga mutane su fita su yi zaben Gwamna a Jihar Edo

- PDP ta jihar Edo ta yi wa Magoya bayanta shelar su fita su kada kuri’a

- Jam’iyyar ta kuma nemi Shugaban kasa ya gargadi Adams Oshiomhole

- PDP ta na zargin tsohon Shugaban jam’iyyar APC na kasa da tada rikici

Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Edo, ta yi kira da babban murya ga ‘ya ‘ya da magoyanta da su shirya fita ranar zaben gwama, su kada kuri’arsu.

Ganin zaben jihar Edo ya na kara gabatowa, PDP ta bukaci mutane su yi kokarin ganin gwamna mai-ci Godwin Obaseki ya zarce a kan mulki.

Bayan haka, jam’iyyar ta PDP ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ja wa tsohon shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole kunne.

PDP ta nemi dinbin magoya bayanta da su yi watsi da dabarun da jam’iyyar APC ta ke neman yi na ganin an hana miliyoyin mutane fitowa su yi zabe.

KU KARANTA: Sanatan APC ya ziyarci Abdussalami ya yi magana game da siyasar 2023

Zaben 2020: PDP ta yi kira ga mutane su fita su yi zaben Gwamna a Jihar Edo
Obaseki ya zargi APC da neman murde zaben Jihar Edo
Source: Twitter

A bangare guda, Hadimin gwamnan jihar Edo, Crusoe Osagie ya fitar da jawabi a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, ya na zargin APC da shirya magudi.

Mista Crusoe Osagie ya ce tun kafin a gudanar da zabe, jam’iyyar APC mai adawa a Edo ta shirya sakamakon zaben bogi domin ta murde kuri’un jama’a.

“Wannan tsohuwar dabara ce ta jam’iyyar APC domin a cirewa jama’a kwarin gwiwar fita su kadawa gwamna Godwin Obaseki kuri’arsu.” Inji Osagie.

A ranar 19 ga watan Satumban nan ne mutanen Edo su ke sa ran cewa za su san wanene zai rike kujerar gwamnan jihar daga 2020 zuwa shekarar 2023.

Mai taimakawa gwamnan ya ce APC ta gudanar da zaben somin-tabi domin ganin yadda abubuwa za su kasance, amma sun ga Obaseki ya fi su farin-jini.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel