COVID-19: ACRI ta hada-kai da HumAngle, ta rabawa Almajirai 2, 300 kaya

COVID-19: ACRI ta hada-kai da HumAngle, ta rabawa Almajirai 2, 300 kaya

Kungiyar nan ta Almajirai Child Right Initiative, ACRI ta agazawa Almajirai sama da 2, 000 a lokacin da aka rufe gari saboda annobar COVID-19.

HumAngle ta fitar da rahoto a jiya ranar Litinin cewa Almajirai 2, 300 a yankin Arewacin Najeriya su ka amfana da kayan tallafn da kungiyar ACRI ta raba.

Shugaban kungiyar ACRI mai kare hakkin Almajirai, Malam Muhammad Sabo Keana ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci ofishi HumAngle a garin Abuja.

Kamar yadda jaridar ta bayyana, Muhammad Sabo Keana ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis da ta gabata, 27 ga watan Agusta, 2020.

Sabo Keana ya bayyana yadda su ka bada gudumuwar a garuruwan Arewa; A jihar Kano, Almajirai 800 aka ba tallafi, a Katsina kuma an taimakawa Almajirai 700.

KU KARANTA: Manyan Arewa sun fadakar da Jama'a kan shirin da Sanatoci su ke yi

COVID-19: ACRI ta hada-kai da HumAngle, ta rabawa Almajirai 2, 300 kaya
Wasu Almajirai a Najeriya
Source: UGC

Haka zalika a babban birnin tarayya Abuja, kungiyar ACRI ta kai wa Almajirai 300 tallafi.

ACRI da HumAngle sun shiga wata yarjejeniya da za su yi aiki da juna, wanda ake sa ran hakan zai taimakawa bangorin biyu wajen gudanar da ayyukansu cikin sauki.

Wani babban jami’in HumAngle, Malam Aliyu Dahiru Aliyu, ya godewa darektan ACRI da wanann ziyara, ya kuma tabbatar masa da cewa za su yi aiki da juna.

Binciken da jaridar ta yi a baya ya nuna yadda Almajirai su ke cikin mawuyacin hali a Najeriya, musamman a lokacin da aka hana zirga-zirga saboda rage yaduwar COVID-19.

Da wannan yarjejeniya, kungiyoyin nan za su kara kokarin ganin gwamnati da sauran hukumomi sun kawowa Almajirai agaji a matsayinsu na ‘yan kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel