Zaben gwamnan Edo: PDP ta bukaci Buhari da ya taka wa Oshiomhole birki

Zaben gwamnan Edo: PDP ta bukaci Buhari da ya taka wa Oshiomhole birki

- Jam'iyyar PDP reshen jihar Edo, ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari a kan ya taka wa Adams Oshiomhole birki domin ya daina rura wutar rikici a jihar

- Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Kabir Adjoto ne ya yi kiran a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta

- Sai dai Oshiomhole da jam’iyyar APC sun karyata zargin

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Edo, ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan ya taka wa tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, (APC), Adams Oshiomhole birki domin ya daina rura wutar rikici a jihar.

Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Kabir Adjoto ne ya yi kiran a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, a Benin yayinda yake jawabi ga manema labarai kan rikicin karamar hukumar Akoko-Edo.

Oshiomhole da jam’iyyar APC sun karyata zargin.

Adjoto ya kuma yi kira ga sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, da ya kafa tawaga domin binciken rikici a yankin don hana ci gaban rikici kan mambobin PDP a yankin.

Adjoto ya ce ‘yan bindiga sun bude wuta a kan magoya bayan PDP a Ekpe a lokacin wani taro a ranar 28 ga watan Agusta, har mutum 13 suka jikkata inda suke samun kulawar likitoci a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Zaben gwamnan Edo: PDP ta bukaci Buhari da ya taka wa Oshiomhole birki
Zaben gwamnan Edo: PDP ta bukaci Buhari da ya taka wa Oshiomhole birki
Asali: UGC

Ya ce harin ba karyar da mutanen ba illa kara masu karfi a hukuncinsu na zabar Obaseki wanda yake tare da mutane.

“Abunda muke so shine zaben lumana inda mutane za su zabi son zuciyarsu. Don haka muna kira ga shugaba Buhari, saboda shi mutum ne mai son zaman lafiya kuma yana da ikon taka wa Oshiomhole birki ya daina tayar da fitina a jihar,” in ji shi.

Da yake martani, kakakin Oshiomhole, Victor Oshioke, ya karyata zargin, inda yake cewa tsohon gwamnan mutum ne mai son zaman lafiya.

Ya ce Oshiomhole na amfani da lallashi, karfin harshe da kokari wajen lashe zabe ba wai rikici ba.

KU KARANTA KUMA: Matsalar tsaro a Arewa: Ka nemi shawarar shuwagabannin Arewa - Sani ya shawarci Buhari

“A dukkanin zabensa, bai taba amfani da rikici ba, me zai sa ya yi amfani da tashin hankali a yanzu.

“Koda Adjoto ya yi karya, ba zai sauya gaskiyar cewa Oshiomhole bai da hannu a tashin hankali ba. Adjoto ne aka sani da rikici a ko ina ya je,” in ji shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel