Ma su garkuwa da mutane sun tare babbar hanya a Kano, kwamandan HISBAH ya sha da kyar

Ma su garkuwa da mutane sun tare babbar hanya a Kano, kwamandan HISBAH ya sha da kyar

- Ma su garkuwa da mutane sun bulla dajin Falgore a karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano

- Sun yi awon gaba da mutane uku a yayin da mutane da dama suka tsira da raunuka

- Daga cikin mutane da suka sha da kyar akwai babban kwamandan HISBAH na karamar hukumar Doguwa

Wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton ma su garkuwa da mutane ne sun tare babbar hanyar zuwa Kano da ta ratsa ta cikin dajin Falgore a karamar hukumar Doguwa.

Shaidar gani da ido, Ado Musa, mazaunin garin Doguwa, ya tabbatarwa da gidan radiyon Freedom faruwar lamarin.

A cewar shaidar, 'yan ta'adda, dauke da muggan makamai, sun tare hanyar Doguwa zuwa cikin birnin Kano da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar Litinin.

Shaidar ya sanar da Freedom cewa 'yan bindigar sun yi awon gaba da wasu mutane uku wadanda har yanzu babu labarinsu.

Ado Musa ya kara da cewa mutane da dama sun samu raunuka sakamakon faruwar lamarin.

Daga cikin wadanda harin ya ritsa da su amma suka tsira da raunuka akwai kwamandan hukumar HISBAH na karamar hukumar Doguwa, Malam Mukhtar Abdulmmumin.

Ma su garkuwa da mutane sun tare babbar hanya a Kano, kwamandan HISBAH ya sha da kyar
Ma su garkuwa da mutane sun tare babbar hanya a Kano, kwamandan HISBAH ya sha da kyar
Asali: Facebook

Babban kwamandan HISBAH na ji ihar Kano, Sheikh Harun Ibn Sina, ya sanar da freedom radiyo cewa lamarin ya ritsa da Malam Abdulmmumin yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa birnin Kano.

DUBA WANNAN: Dadiyata: Gwamnatin Kaduna ta yi magana a kan bacewar barden Kwankwasiyya

Sheikh Ibn Sina ya kara da cewa yanzu haka kwamanda Malam Abdulmmumin ya na samun kulawa a asibiti.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kara da cewa rundunar 'yan sanda ta fara bincike a kan faruwar lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel