Yanzu Yanzu: Osinbajo ma ya hallara yayinda Fasto Adeboye ya gana da Buhari a Aso Rock
- Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) Fasto Enoch Adeboye ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a fadar Villa
- Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ma sun halarci ganawar wanda aka yi a sirri
- Sun fara ganawar da misalin karfe 3:00 na rana a ofishin shugaban kasar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, ya gana da shugaban cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) Fasto Enoch Adeboye.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa sun fara ganawar da misalin karfe 3:00 na rana a ofishin shugaban kasar.
Zuwa yanzu dai ba’a san cikakken abunda taron nasu ya kunsa ba.
Cikin wadanda suka halarci taron wanda aka yi cikin sirri harda mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
KU KARANTA KUMA: Sarkin Oyo ya bayyana yadda aka yi ya tara mata da yawa

Asali: UGC

Asali: UGC

Asali: UGC
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng