Yanzu-Yanzu: An gudanar da gagarumin zanga-zanga a birnin Minna saboda rashin wutar lantarki

Yanzu-Yanzu: An gudanar da gagarumin zanga-zanga a birnin Minna saboda rashin wutar lantarki

- Fusatattun matasan yankin Kpakungun da ke Minna, a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, sun toshe manyan hanyoyin Minna, babbar birnin jihar Neja domin zanga-zanga

- Suna zanga-zanga ne a kan rashin samun isasshen wutar lantarki

- Duk kokari da gwamnatin jihar ta yi na ganin masu zanga-zangar sun kawo karshen shirin ya ci tura yayinda SSG ya yi gaggawan barin wajen bayan ihun da aka masa

- Sun bukaci lallai Gwamna Abubakar Sani Bello ya zo da kansa ko su toshe hanyar na tsawon sa'o'i 24

Matasan yankin Kpakungun da ke Minna, a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, sun toshe manyan hanyoyin Minna, babbar birnin jihar Neja domin zanga-zanga a kan rashin wutar lantarki a birnin.

Fusatattun matasan sun kuma kora babban sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Matane, wanda ya roke su a kan su bude manyan hanyoyin da kuma dakatar da zanga-zangar.

Sun bukaci Gwamna Abubakar Sani Bello da ya bayyana a wajen domin ya yi masu jawabi.

Matasan sun kaddamar da cewar sun gaji da gurguntaccen wutar lantarki da ake basu, cewa kamfanin wuta na Abuja (AEDC) ta wofantar da al’umma.

KU KARANTA KUMA: Komawa garin Azare da zama: Sanusi Lamido Sanusi ya magantu

Yanzu-Yanzu: An gudanar da gagarumin zanga-zanga a birnin Minna saboda rashin wutar lantarki
Yanzu-Yanzu: An gudanar da gagarumin zanga-zanga a birnin Minna saboda rashin wutar lantarki
Source: Twitter

Hanyar Kpakungun shine hanya guda da ke sada mutane da yankunan kudancin kasar kuma ya kasance daya daga cikin manyan hanyoyin da aka fi amfani da su a jihar.

Masu mota musamman wadanda ke tafiya kudu sun yi cirko-cirko a hanyar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Duk kokari da gwamnatin jihar ta yi na ganin masu zanga-zangar sun kawo karshen shirin ya ci tura yayinda SSG ya yi gaggawan barin wajen bayan ihun da aka masa.

Daya daga cikin kansilolin da ke wakiltan unguwar Minna ta Kudu, Aminu Ladan, ya fada wa masu kawo rahoto cewa babu wani bayani daga hukumomi, cewa zanga-zangar ya gudana cikin lumana.

“Kamar yadda kuke gani, an kori SSG cikin fushi kuma bai yi nasarar isar da sakon da ya kawo ba. Mutanena na son gwamna ya bayyana.

“A matsayina na wanda ke rike da mukamin siyasa, na san cewa SSG wakilin Gwamna ne amma mutanen basu fahimci haka ba. Basu gamsu ba kuma suna son Gwamna ya zo da kansa,” in ji shi.

Matasan sun sha alwashin rufe hanyar na tsawon sa’o’i 24 har sai gwamnan ya bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel