La-liga: Lionel Messi zai iya barin Barcelona idan har ya bada fam €700m

La-liga: Lionel Messi zai iya barin Barcelona idan har ya bada fam €700m

Hukumar La-liga ta ce Lionel Messi zai iya barin kungiyar Barcelona ne kawai idan aka biya makudan kudin da ke cikin sharadin kwantiraginsa.

A ranar Lahadi, 30 ga watan Agusta, 2020, La-liga ta yi magana game da ce-ce-ku-cen da ake yi game da yiwuwar tashin Lionel Messi daga kungiyar Barcelona.

A cewar hukumar kwallon kafan, sai ‘dan wasan ya ajiye Dala miliyan 823 (ko kuma fam miliyan €700 ko £624) idan zai tashi daga kungiyarsa kafin karshen badi.

Lauyoyin Lionel Messi su na ikirarin cewa sharadin kwantiragin ‘dan wasan ya kare a watan Yuni, don haka su ke ganin ya na da hurumin da zai canza sheka.

Gardamar da ake yi ita ce annobar COVID-19 ta sa an tsawaita kakar bana zuwa Agusta.

Manchester City ce ake ganin za ta saye shahararren ‘dan wasan. A jiya hukumar kwallon kafa ta La-liga ta ce kwantiragin ‘dan wasan ya na aiki har zuwa 2021.

KU KARANTA: Man City ta na harin Lionel Messi

La-liga: Lionel Messi zai iya barin Barcelona idan har ya bada fam €700m
Lionel Messi ya na so ya tashi dag Barcelona
Asali: Getty Images

Abin da wannan sanarwa ta ke nufi shi ne dole sai an samu wanda zai biya kudin da ke kan Lionel Messi kafin ya samu damar barin Barcelona a kakar shekarar nan.

Idan aka yi lissafi, wadannan makudan kudi sun haura Naira Biliyan 390. Duk kungiyar da ke son raba Messi da Barcelona, sai ta yi kashin wadannan kudi kafin ta dauke shi.

Jawabin hukumar ta ce: “Game da mabanbantan fahimtar da ake samu a ‘yan kwanakin nan game da lamarin Messi da Barcelona. La Liga ta na ganin ya kamata ta yi karin haske."

“Kwantiraginsa ya na ci, kuma ya na dauke da sharadin tashi wanda zai yi aiki idan har Lionel Messi shi kadai ya bukaci sai ya bar kungiyar kafin lokaci ya yi.” Inji La-liga.

Rahotanni daga kasar Sifen sun tabbatar da cewa har yanzu an gaza shawo kan Lionel Messi. ‘Dan wasan ya ki zuwa wasa, sannan ya ki bari ayi masa gwajin cutar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng