Shugaban ‘yan sanda ya gargadi ‘yan siyasa a kan tayar da rikici lokacin zabukan Edo da Ondo

Shugaban ‘yan sanda ya gargadi ‘yan siyasa a kan tayar da rikici lokacin zabukan Edo da Ondo

- Shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya gargadi 'yan siyasa a jihohin Ondo da Edo da su shiga hankalinsu yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna

- Za a gudanar da zabuka a Edo da Ondo a ranar 19 ga watan Satumba da 10 ga watan Oktoba

- Sufeton ya yi wa 'yan siyasar da magoya bayansu gargadin cewa su bi doka kuma su guji duk abin da zai jawo tashin hankali

Gabannin zabukan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana yiwuwar barkewar rikici, hare-hare daga abokan adawa, da kuma watsa bayanan karya a matsayin babban barazanar tsaro ga zabukan.

An shirya gudanar da zabuka a Edo da Ondo a ranar 19 ga watan Satumba da 10 ga watan Oktoba.

Sufeto janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu ya gargadi ‘yan siyasa da magoya bayansu da su kama kansu sosai ta hanyar bin doka.

Shugaban ‘yan sanda ya gargadi ‘yan siyasa a kan tayar da rikici lokacin zabukan Edo da Ondo
Shugaban ‘yan sanda ya gargadi ‘yan siyasa a kan tayar da rikici lokacin zabukan Edo da Ondo
Asali: Facebook

Ya kuma shawarce su da su guji duk wani abu da ka iya kawo matsala a gudanarwar zabe a jihohin biyu.

A wani jawabi daga kakakin ‘yan sandan, Frank Mba, ya ce shugaban rundunar ya yi gargadin ne bayan ya sake duba rahoton matsalar tsaro a zaben wanda kwamishinonin ‘yan sanda na jihohin biyu suka gabatar a wani taro da aka gudanar a ranar Talata, 25 ga watan Agusta.

KU KARANTA KUMA: Amaechi ya ce za a kammala jami’ar sufuri na Daura a 2021

Ya kara da cewar shugaban yan sanda yana shirya wani tsarin tsaro domin kare mutane da tabbatar da zabukan lumana.

Ya ci gaba da cewa rundunar za ta tabbatar da doka a kan kowa ba tare da la’akari da matsayin duk wanda ya yi kokarin kawo tsaiko a tsarin tsaro.

Tuni lamuran siyasa suka dauki zafi musamman a Jihar Edo, inda gwamna Obaseki ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki kuma ya koma PDP sakamakon hana shi tikitin yin ta-zarce da jam'iyyar ta yi.

Rikicin siyasar har ya kai ga an tsige kakakin majalisar dokokin jihar tare da maye gurbinsa da wani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng