Hira da mahaifin jaruma Fadila Muhammad: Ya bayyana ciwon da ya kasheta
Mutuwar sananniyar jarumar Kannywood, Fadila Muhammad, a daren Juma'a ya matukar girgiza zukatan jama'a a masana'antar fina-finai.
Mujallar Fim ta tabbatar da cewa, jarumar ta rasu a daren Juma'a, 28 ga watan Augustan 2020 da misalin karfe 11 na dare a cikin motar mahaifinta yayin da yake kokarin kaita asibiti.
Tuni dama jarumar na fama da ciwon zuciya, kuma tun a ranar a ranar Alhamis ciwon ya tashi. An mika ta sibiti inda ta samu sauki kuma aka mayar da ita gida a ranar. Ciwon ya sake tashi, wanda bai sake lafawa sai dai tafiya da ranta da yayi.
Jarumar mai shekaru 27 a duniya an yi mata sallar jana'izarta da misalin karfe 8:30 na safiyar Asabar a gidan iyayenta da ka fagge Close, Unguwar Dosa da ke Kaduna.
Marigayiyar ta kai kimanin shekaru 8 a masana'antar Kannywoo inda ta yi fina-finai da dama. Ta fito a fim din Basaja da kuma Hubbi, a wadannan fina-finan ne ta shahara.
Mujallar fim ta halarci jana'izar jarumar kuma ta samu zantawa da mahaifinta wanda ke cike da alhinin rashinta.
KU KARANTA: Lauyan da yayi murnar mutuwar Kyari da Funtua, da fatan mutuwar Buhari ya rasu
Malam Muhammad ya ce, "Lallai wannan rashi ne da muka yi amma babu abinda zan ce sai Allah ya jikanta da rahama. Yasa Aljannar Firdausi makoma gareta," yana fadin hakan yana kuka.
Ya kara da cewa, "Wannan yarinyar babu abinda zan ce mata sai Allah ya saka mata da alheri tare da gidan Aljanna.
"Tana yi min biyayya, Allah na gode maka da ka amshi ranta a hannuna."
Ya kara da cewa, "A kullum addu'ar ta Allah ya karba rayuwarta kafin nawa, domin bata son in rasu in barta. Abinda zan dinga tuna ta da shi shine, kullum burinta ta yi min abinda zai kawo min saukin rayuwa."
A take ya sake fashewa da kuka. Ya bada sako inda yake bukatar duk mai binta bashi a cikin abokan aikinta da ya bayyana kansa.
Bayan tuntubar shugabar kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta kasa, reshen jihar Kaduna, Hajiya Fatima Ibrahim, ta bayyana tsananin tashin hankalinta a kan wannan rashin na Fadila.
Ta bayyana cewa, daga iyayen Fadila a jin mutuwar sai ita, domin kuwa ta hannunta ne ta shiga masana'antar kuma tamkar uwa take gareta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng