Buhari: Attah na Igala, Ameh Oboni II, mutum ne mai son zaman lafiya

Buhari: Attah na Igala, Ameh Oboni II, mutum ne mai son zaman lafiya

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Attah na Igala, Micheal Idakwo Ameh Oboni II a matsayin mutum mai son zaman lafiya.

Shugaban kasar, cikin sanarwar da mai magana da yawun bakinsa, Garba Shehu, ya mika ta'aziya ga iyalai, abokai da yan uwan mai martaban bisa rasuwarsa.

Ya kuma yi wa majalisar masauratar Kogi da gwamnatin jihar ta'aziya bisa rasuwar fitaccen basaraken na Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana marigayin a matsayin "mutum mai son zaman lafiya da ya sadaukar da rayuwarsa wurin kawo hadin kai da cigaba da al'ummarsa da ma kasa baki daya."

Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar Attah na Igala
Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar Attah na Igala
Source: Twitter

Buhari ya ce za ayi kewar Attah na Igalan na 27 matuka ta musamman shawarwari da gaskiya da hikima da aka san shi da shi, ya bukaci mutanen kasarsa su dora a kan ayyukan da ya yi a mulkinsa na shekaru takwas.

Shugaban kasar ya yi adduar Allah ya bawa iyalan mammacin hakurin jure rashinsa ya kuma sa ya huta.

Dan Attah na Igala, Yarima Ocholi Idakwo, a safiyar Asabar ne ya sanar da rasuwar sarkin mahaifinsa a hukumance.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Yadda wani mutum ya riƙa kuka yana birgima cikin taɓo don budurwarsa ta ƙi yarda ta aure shi

Hakan na zuwa ne kimanin awa 24 bayan lauyoyin marigayin sarkin sun nuna rashin jin dadin su kan yadda kafafen watsa labarai suka sanar da rasuwarsa.

Yariman ya sanar da rasuwar sarkin a hukumance a fadarsa yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi.

A cikin sanarwar da kakakinsa, Dakta Gabriel Ottah ya sanar, Yarima Ocholi, ya tabbatar da cewa Attah ya riga mu gidan gaskiya a ranar 27 ga watan Agustan shekarar 2020.

Ya yi wa alumma godiya bisa goyon baya da cigaban da suke ba su.

Yarima Ocholi ya bayyana mahaifinsa a matsayin mutum da baya wasa da aiki da ya mayar da hankali wurin inganta al'adun Igala.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel