Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

Fasto Emmanuel Nuhu Kufe na babbar cocin Throneroom da ke Kafanchan, ya ce jama'a na zuwa wurinsa da bukatar ya siya musu makamai don kare kansu.

"Suna kira ga fastoci da su dauka wani bangare na kudin baikonsu don siyan makamai don bai wa kansu kariya. A halin yanzu jama'a basu tsoron komai," in ji shi.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi maganin zubar jinin da ke faruwa a yankin kudancin Kaduna kafin ya janyo wata matsala daban.

Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu
Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

A yayin jawabi ga mazauna yankin kudancin Kaduna a cocin ECWA da ke Kaduna, ya ce lamarin da ke faruwa a halin yanzu matukar ba a shawo kan shi ba zai iya kawo juyin juya hali inda jama'a za su fito suna bai wa kansu kariya.

Ya ce duk da sojin da gwamnatin tarayya suka tura, har yanzu ba a daina zubar da jini a yankin ba.

"Ina kira ga gwamnatin tarayya da dukkan shugabanni da su duba wannan matsalar da fuskar fahimta. Yankin kudancin Kaduna na jiran matakin da zai samarwa jama'a zaman lafiya."

"A karon farko a rayuwata, ina son sanar da Fulani cewa sun yi martanin da suke so don haka su bar jama'ar kudancin Kaduna. Muna cikin matsanancin hali."

"Duk da Fulani basu da shugabannin, da suna da su da sun hana su abinda suke yi a kudancin Kaduna."

DUBA WANNAN: Bidiyo: Yadda wani mutum ya riƙa kuka yana birgima cikin taɓo don budurwarsa ta ƙi yarda ta aure shi

"Ina kalubalantar shugabannin Fulani da su samo hanyar shawo kan matsalolin su. Su hadu da shugabanninsu da suke da ilimi ba wadanda basu da shi ba. Ya kamata su sani cewa dukkan kabilun Najeriya 'yan kasar nan ne kuma suna da hakki."

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran 'yan siyasa ya kamata su daina kare Fulani idan har suna son shawo kan matsalar kasar nan da kuma rikicin Kaduna."

Kure, wanda sakataren PFN na kasa ne ya jajanta yadda wasu daga cikin jami'an gwamnati da aka saka domin kawo sasancin suke yi da wata manuga. Ya bukacesu da su shiga harkar saboda bukatar kawo zaman lafiya a jihar.

Ya yi kira ga gwamnati da ta bada damar tattaunawa da 'yan kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel