Ina caccakar sojoji ne domin na taimake su wajen kara zage damtse, in ji Zulum

Ina caccakar sojoji ne domin na taimake su wajen kara zage damtse, in ji Zulum

Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya ce yana sukan rundunar sojin Najeriya ne saboda su inganta yaki da suke da ta’addanci.

Zulum ya bayyana hakan a ranar Alhamis lokacin da ya kaddamar da cibiyar Tukur Buratai na yaki da zaman lafiya, wanda ke karamar hukumar Biu na jihar.

An sanya wa cibiyar sunan Tukur Buratai, shugaban hafsan soji.

Gwamnan ya caccaki rundunar soji a kwanakin baya.

A watan Janairu, ya zargi dakarun soji da tatsar masu amfani da hanyoyi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa jarumar Kannywood Fadila Muhammad rasuwa

Ina caccakar sojoji ne domin na taimake su wajen kara zage damtse, in ji Zulum
Ina caccakar sojoji ne domin na taimake su wajen kara zage damtse, in ji Zulum
Asali: Twitter

Ya kuma yi barazanar maye gurbin sojoji da maharba idan suka gaza tsare Bana biyo bayan harin da aka kai masa a watan Yuni.

Yayinda aka yarda cewa yan ta’addan Boko Haram ne suka kai harin, Zulum ya zargi jami’an sojiji da zagon kasa, inda ya yi zargin cewa sune suka kai masa hari.

Sai dai, rundunar sojin ta bukaci Zulum da ya dakatar da batawa rundunar suna a furucinsa.

Da yake magana a taron kaddamarwar, Zulum ya ce ba wai baya godema kokarin sojojin bane.

Ya yi bayanin cewa, maimakon haka, zafafan zantuntuka da yake lokaci-lokaci domin karfafa masu gwiwar kara kaimi ne.

“Ba wai bana sane da inda muke bane kafin kafuwar shugabancin Buratai bane da kuma nasarorin rundunar soji wajen yaki da ta’addanci. Muna godiya da sadaukarwar rayuka da dakarun soji ke yi. Za mu ci gaba da marawa sojojinmu baya,” in ji Zulum.

“Idan muka sokesu lokaci zuwa lokaci, muna hakan ne domin inganta nasarorinmu ba wai rashin godiya bane.”

Cibiyar wani sashi ne na jamiyar rundunar sojin Najeriya wacce ke a garin Biu.

Da farko shine wajen ajiyen kayan tarihi na rundunar soji na kasa, an samar da shi a 2016.

KU KARANTA KUMA: Kungiya ta bayyana jerin sunayen ‘yan siyasa 11 da take so su zama shugaban kasa a 2023

Gwamnan ya yi bayanin cewa cibiyar zai bunkasa bincike kan lamura kamar su ta’addanci da duk wasu rikici ta fuskacin samun zaman lafiya.

Ya bayyana cewa an rage tasirin ta’addanci a jihar sannan kuma ya sha alwashin cewa a shirye gwamnatinsa take ta hada kai da cibiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng