Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa jarumar Kannywood Fadila Muhammad rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa jarumar Kannywood Fadila Muhammad rasuwa

Allah ya yi wa fatacciyyar jarumar Kannywood Fadila Muhammad ta rasu. Ta rasu ne a daren ranar Juma’a, 28 ga watan Agusta.

Kafin mutuwarta jarumar ta fito a fina-finai da dama da suka hada da Basaja, Bikin Yar Gata, Hubbi, Karfen Nasara, Mai Farin Jini, Na Hauwa da dai sauransu.

Tuni manyan jaruman masana’antar suka fara nuna alhini da juyayi na rashin wannan abokiyar sana’arsu da suka yi a shafukansu na Instagram.

KU KARANTA KUMA: Kungiya ta bayyana jerin sunayen ‘yan siyasa 11 da take so su zama shugaban kasa a 2023

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa jarumar Kannywood Fadila Muhammad rasuwa
Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa jarumar Kannywood Fadila Muhammad rasuwa Hoto: Fati KK
Source: Instagram

Maryam Booth ta wallafa: “Inna lillahi wa inna ilayhir rajiun Inna lillahi wa inna ilayhir rajiun Innalillaywa inna ilayhir rajiun Ubangiji Allah yajiqan ki Farida."

Teemah Yola: “Allah ya jikanta da rahama Ameen ya rabbi.”

Ummah Shehu: “Innalillahi wa’inna’ilaihir raju’un allah yayiwa fadila rasuwa yanzu Allah yajikanki da rahama yasa mutuwa hutune agareki ya yafe miki dukkan kurakuranki amin.”

Rikadawa: “Innalillahi Wa Inna'ilaihirraji'un!!! Allah ya jikan ki da Rahma ya yafe miki kurakuren ki. Amin."

Aysha Sarki: “Allah yajikanki da rahama fadeela Allah yayi miki rahama Allah yasa annabi yaceceki Allah ya kyautata namu zuwan.”

Fati KK: "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Allah yayi maki rahma ummi,Allah yasa Aljanna ce makomaYa rabbi"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel