Mutane 16, 500 sun sa hannu a korafin Hadimin Jonathan na binciken Bola Tinubu
Sama da mutane 16, 000 su ka sa hannu a wani korafi zuwa ga hukumar EFCC da ta gudanar da bincike a kan jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu.
Wadannan mutane da adadinsu ya haura 16, 500 a yammacin Juma’a, 28 ga watan Agusta, su na neman a binciki zargin da ke kan tsohon gwamnan na Legas.
Hadimin tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan, Reno Omokri shi ne ya fara wannan kira, inda ya gayyaci mutane a dandalin sada zumunta na zamani.
Reno Omokri ya shirya wannan kiran korafi ne a shafin yanar gizo na Change.Org. Bisa dukkan alamu wannan korafi ya na cigaba da samun karbuwa ta ko ina.
An yi wa korafin taken, ‘Kira ga EFCC ta binciki Bola Tinubu saboda sabawa dokar haramta safarar kudi ta shekarar 2011 ta shigo da manyan motoci dauke da makudan kudi a gidansa a jajibirin zaben shugaban kasa na 2019.’
Omokri ya yi karin bayani, ya rubuta, “Ya ku al’ummar Najeriya, mu karbe kasarmu ta hanyar sa hannu a wannan korafi da zai tursasawa hukumar EFCC binciken Bola Tinubu."
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari na shirin biyan malaman da ba su samun albashi
Bayan haka, Omokri ya kara da kiran jama’a cewa ka da su tsaya su na cewa ‘Ba yau aka fara ba’ ko ‘a bar maganar’.
“Ni da kai za mu iya kawo banbamci ta hanyar rattaba hannumu a kan korafin nan.” #EFCCMustInvestigateTinubu.”
“A matsayinmu na ‘yan Najeriya mu daina daukar rashin yarda da hikima. Idan ba mu yi yaki domin kasarmu ba, wa zai yi?” Fasto Reno Omokri ya jefa tambaya.
Ba yau aka fara kiran hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta binciki wannan zargi ba, amma har yanzu babu abin da aka ji.
Da aka nemi jin ta bakin Tinubu a wancan lokaci, sai ya ce ya na da damar rabawa jama’a duk kudin da ya ga dama tun da ya ba rike da wata kujera a gwamnati.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng