Man City ta na harin Lionel Messi, ‘Dan wasa ya na magana da Pep Guardiola

Man City ta na harin Lionel Messi, ‘Dan wasa ya na magana da Pep Guardiola

Ana cigaba da rade-radin kungiyar Manchester City ta na zawarcin Lionel Messi. Abubuwan da za su taimakawa cinikin sun hada da kudi, sanayya da karfin kungiyar.

Jaridar The Sun ta ce maganar komawar Lionel Messi zuwa Manchester City inda zai hadu da tsohon mai gidansa a Barcelona watau Pep Guardiola, ta na kara karfi.

Lionel Messi ya sanar da Barcelona shirinsa na tashi daga kungiyar da ya ci wa kwallaye 634. Fitaccen ‘dan kwallon na kasar Argentina ya buga wasanni fiye da 700.

‘Dan wasa Messi da Koci Guardiola sun ji dadin tarayyar da su ka yi a Barcelona, inda su ka yi nasarar lashe gasa 14 tsakanin shekarar 2008 zuwa karshen kakar 2012.

Kungiyoyin Duniya sun fara yin ca a kan Messi tun da ya fito ya bayyana shirinsa na barin Barcelona. Daga cikin masu zawarcinsa akwai PSG, City, da kuma Inter.

Paris Saint-Germain da Bayern Munich da su ka kara wajen gasar cin kofin Turai sun fita daga cikin masu neman ‘dan wasan bayan sun ji labarin makudan albashinsa.

KU KARANTA: Ronaldo ya aikawa Magoya bayan Juventus sako a Instagram

Man City ta na harin Lionel Messi, ‘Dan wasa ya na magana da Pep Guardiola
Messi ya shaidawa kungiyarsa shirin da ya ke yi na barin kulob
Asali: UGC

Dole kungiyar da za ta saye ‘dan wasan ta yi hankali da dokar FFP na cefanen ‘yan wasa. Hukumar UEFA ta kawo dokar domin hana kungiyoyi kashe kudin da ya fi karfinsu.

Idan har Pep Guardiola ya yi nasarar jan ra'ayin Messi, ya na da ‘yan wasa da-dama da Manchester City za ta sa a kasuwa domin a maida bangaren kudin da ta kashe.

Bayan City, kungiyar Inter Milan ta Italiya, ta na sha’awar Lionel Messi tun ba yau ba. Masu hasashe su na ganin ‘dan wasan gaban zai fi jin dadin ya yi aiki da tsohon kocinsa.

Manchester Cty ta kashe makudan kudi amma har yanzu ta gaza yin fice a Turai, kawo ‘dan wasan mai shekara 33 wanda ya lashe Ballon D’or har sau shida zai taimaka.

Txiki Begiristain wanda yanzu ya ke rike da mukamin darektan wasanni a City, tsohon mutumin Barcelona ne, wannan alaka za ta iya taimakawa tsofaffin zakarun na Ingila.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel