Da duminsa: Kwamishina ta yi murabus kan zargin karkatar da N300m a Kwara

Da duminsa: Kwamishina ta yi murabus kan zargin karkatar da N300m a Kwara

Kwamishiniyar ayyuka na musamman ta jihar Kwara, Hajia Aisha Ahman Pategi, ta yi murabus daga mukarraban gwamna AbdulRahman AbdulRazq biyo bayan zargin karkatar da N300m na kananan hukumomin jihar.

Da ya ke tabbatar da murabus din kwamishiniyar, kwamishinan watsa labarai, Harriet Afolabi-Oshatimehin a cikin wata sanarwa ya yi mata fatan alkairi a ayyukanta na gaba.

Sanarwar na cewa, "Gwamnati ta karbi takardar murabus din Hon. Aishah Ahman-Pategi wacce ta kasance kwamishiniyar ayyuka na musamman.

"Gwamnati ta amince da wannan murabus, a lokaci daya kuma tana yi mata fatan alkairi a rayuwara, da ayyukanta."

Hajiya Pategi ta kasance tsohuwar kwamishiniyar kananan hukumomi da harkokin masarautu ta jihar a lokacin da batu kan karkatar da kudaden ya fara tasowa.

A lokacin, gwamnan jihar ya mayar da ita kwamishiniyar ayyuka na musamman biyo bayan rikicin da ya soma tashi tsakaninta da kwamishiniyar kudi, Mrs Florence Oyeyemi.

KARANTA WANNAN: NYSC ta fadi lokacin da zata bude sansanonin horas da matasa masu yiwa kasa hidima

Da duminsa: Kwamishina ta yi murabus kan zargin karkatar da N300m a Kwara
Da duminsa: Kwamishina ta yi murabus kan zargin karkatar da N300m a Kwara
Source: Twitter

Mrs Florence Oyeyemi na tuhumar Pategi akan dalilin da ya sa ta cire kudaden kananan hukumomin ba tare da bin ka'idojin hakan ba, da kuma son sanin me akayi da kudaden.

A cewar wasikar murabus da ta aikewa gwamnan, mai dauke da kwanan wata 28 ga watan Agusta 2020, ta godewa Allah da ya bata ikon yin aiki har zuwa wannan lokaci, ta kuma godewa gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da damar da ya bata.

Tuni dai gwamna AbdulRazaq ya kafa kwamiti da zai yi bincike kan sama da fadi da kudaden kananan hukumomin, bisa jagorancin mai shari'a Matthew Adewari.

Sai dai da yawa daga cikin masu ruwa da tsaki na mulkin kananan hukumomin sun i babu wasu kudi da aka karkatar ba kamar yadda ake zargi ba.

Haka zalika, shugaban kwamitin binciken, wanda ke ci gaba da aiki, mai shari'a Adewara ya koka kan yadda babu wasu takardu da kwamitin ke samu daga al'ummar jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel