An sace matashi, dan sanda, da 'Civil Defence' a Kaduna

An sace matashi, dan sanda, da 'Civil Defence' a Kaduna

Ma su garkuwa da mutane sun sace wani jami'in hukumar tsaro ta NSCDC (civil defence) da kuma wani dan sanda a jihar Kaduna.

A cewar wani shaidar gani da ido, lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na daren ranar Alhamis a yankin Maraban Rido da ke cikin birnin Kaduna.

Kazalika, shaidar ya bayyana cewa 'yan bindigar da su ka sace jami'an tsaron sun sake kai farmaki gidan Mista Elijah Dreams, shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

Mista Dreams ya bayyana cewa 'yan bindigar sun yi awon gaba da karin wasu mutane biyu da suka hada da wata matashiya.

Ya bayyana cewa 'yan bindigar sun budewa gidansa wuta domin samun damar karya kofar gidan, amma duk da haka basu samu nasarar shiga gidan ba.

Ya bayyana takaicinsa a kan yadda al'amarin garkuwa da mutane ke kara yawa a yankin, lamarin da yasa mazauna yankin ke zaune cikin tsoro da fargaba.

"Ma su garkuwa da mutane sun zo gidana da tsakar daren ranar Alhamis tare da yunkurin karya kofar shiga gidana. Sun harbi kofar gidana domin ta karye su samu damar shiga gidana amma sai Allah ya kareni, su ka kasa karya kofar," a cewarsa.

An sace matashi, dan sanda, da 'Civil Defence' a Kaduna
An sace matashi, dan sanda, da 'Civil Defence' a Kaduna
Source: Twitter

Sannan ya kara da cewa; "sun sace jami'in hukumar NSCDC, dan sanda, matashiya mai shekaru 14 da kuma wani mutum guda daya.

DUBA WANNAN: Matawalle ya tona asirin sabuwar hanyar da ake amfani da ita wajen safarar makamai zuwa Zamfara

"A yayin da 'yan bindigar ke cikin ofireshon a unguwrmu, na kira kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na sanar da shi, shi kuma ya sanar da 'yan sanda, amma har 'yan ta'addar suka gama suka tafi babu jami'an tsaron da suka zo."

Jaridar TheCable ta yi kokarin jin ta bakin Mohammed Jalige, kakakin rundunar 'yan sanda a Kaduna kwamand, amma wayarsa a kashe lokacin da aka kira.

Faruwar lamarin na zuwane a cikin kwanaki hudu bayan wasu 'yan bindiga sun kutsa cikin wata makaranta tare da sace dalibai ma su shirin rubuta jarrabawa a makarantar sakandire mallakar gwamnati da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel