Matawalle ya tona asirin sabuwar hanyar da ake amfani da ita wajen safarar makamai zuwa Zamfara

Matawalle ya tona asirin sabuwar hanyar da ake amfani da ita wajen safarar makamai zuwa Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana cewa yanzu 'yan bindiga sun koma amfani da Rakuma wajen safarar makamai zuwa cikin arewacin Najeriya.

Matawalle ya fadi hakan ne a gaban Firaministan kasar Nijar, Brigi Refini, yayin tattaunawa a kan yadda za a dakatar da aiyukan ta'addanci a kan iyakokin yankin Najeriya da Nijar.

Kasar Nijar tana da iyaka mai yawan gaske da Najeriya ta jihar Zamfara.

"Mun san cewa masu safarar makamai ta motoci da ababen hawa sun shiga damuwa sakamakon rufe iyakokin kasa, wannan matsin lamba yasa sun koma amfani da Rakuma domin safarar makamai zuwa Najeriya," a cewar Matawalle.

Sanna ya kara da cewa; "bayan na'urorin leken asiri da muka samar, na dauki alkawarin samar da wasu manyan motoci na musamman da za a ke amfani da su wajen sintiri domin inganta tsaro a kan iyakokinu.

Kazalika, ya mika sakon babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, zuwa Firaminista Refindi a kan bukatar tsohe dukkan hanyoyin da ake amfani da su wajen sfarar makamai zuwa cikin Najeriya.

Matawalle ya tona asirin sabuwar hanyar da ake amfani da ita wajen safarar makamai zuwa Zamfara
Matawalle
Asali: UGC

An gudanar da taron ne domin tattaunawa a kan yadda za a hada karfi a tsakanin gwamnatocin Najeriya da Nijar domin tafiya a turba guda wajen yakar 'yan ta'adda da ta'addanci.

DUBA WANNAN: Soyinka ya caccaki shugaba Buhari a kan shirin kirkirar wata sabuwar doka a Najeriya

Gwamna Matawalle ne ya karbi bakuncin Refini a fadar gwamnatin jihar Zamfara da ke Gusau yayin da ya iso Najeriya domin halartar taron kasa da kasa da aka fara domin tattauna hanyoyin hada kai domin yaki da ta'addanci a tsakanin kasashen biyu.

Refini ya bayyana cewa ba Najeriya kadai ke fama da matsalar rashin tsaro ba, kasarsa ta Nijar ma tana fama da matsalar rashin tsaro ta fuskoki da dama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng