Buhari: Amotekun ba za su zauna karkashin Sufetan ‘Yan Sanda ba inji Makinde

Buhari: Amotekun ba za su zauna karkashin Sufetan ‘Yan Sanda ba inji Makinde

Seyi Makinde ya sha ban-ban da shugaban kasa a game da yunkurin maida dakarun tsaron Operation Amotekun karkashin Sufeta janar na ‘yan sanda.

Gwamnan na jihar Oyo ya ce jami’an tsaron su na da hurumin aiki a dokar jiha, don haka za su yi aiki ne a karkashin gwamnatin jihar ba tare da gwamnatin tarayya ba.

Jaridar Punch ta rahoto Injiniya Seyi Makinde ya na cewa gwamnatinsa ba za ta sallamawa rundunar ‘yan sandan Najeriya ko gwamnatin tarayya jami’an Amotekun ba.

Makinde ya yi jawabi ne ta bakin babban sakatarensa na ya labarai, Taiwo Adisa, a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, 2020, bayan ya gana da shugabannin kananan hukumomi.

Adisa ya rahoto mai gidansa ya na cewa: “Mu na so mutanenmu su yi barci har da minshari, babu shakka tsaro ya na cikin manyan abaubuwan da ke gaban wannan gwamnati.”

“Kuma za mu yi duk abin da za mu iya na ganin mun kare dukiya da rayuka.” Inji Gwamnan.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ba ta yi karin kudin wuta ba – NERC

Amotekun ba za su zauna karkashin Sufetan ‘Yan Sanda ba inji Makinde
Makinde ya musanya maganar Garba Shehu
Asali: Twitter

Makinde ya gana da shugabannin mazabu da kananan hukumomi 68 na jihar Oyo ne a garin Ibadan dazu.

“A Okeho, kwanaki ‘yan fashi sun shiga za su yi barna, mutanen gari su ka tashi tsaye su ka kama su. Su ka laluba daji su ka kamo su.” A cewar Gwamnan na jihar Oyo

Ya cigaba da cewa: “Wannan ya sa zan cigaba da fada kuma ina so Duniya ta ji, babu ranar tafiyar Amotekun. Sannan ba za ta zama karkashin kulawar gwamnatin tarayya ba.”

Mai girma Makinde ya jaddada maganarsa, “Za ta zama karkashin kularmu. Tsaron mutanenmu ya na da matukar muhimmanci, babu abin da zai yiwu muddin akkwai rashin tsaro.”

Gwama Makinde ya yi kira ga shugabannin su koma garuruwansu, su kafa kwamitocin tsaro, ya ce yayin da ake dosar karshen shekara, za a ga karuwar laifuffuka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng