Bahaushiya yar Gombe ta fantsama yanar gizo neman mijin aure

Bahaushiya yar Gombe ta fantsama yanar gizo neman mijin aure

- Wata matashiyar Bahaushiya da ke tsananin neman mijin aure ta je dandalin soshiya midiya domin gwada sa’arta

- Matashiyar budurwar mai suna Salmerh Umar ta ce ita ‘yar jihar Gombe ce

- Salmerh ta ce ba za ta iya ci gaba da boye yadda take ji ba, inda ta bukaci ‘yan Najeriya da su taya ta da addu’a

Wata matashiyar budurwa Bahaushiya da aka ambata da suna Salmerh Umar ta je shafin zumunta domin neman mijin aure yayinda ta bukaci ‘yan Najeiya a Twitter da su taya tad a addu’a.

Matashiyar budurwar wacce shafinta na Twitter yake a matsayin @SalmerhUmar ta ce ba za ta iya ci gaba da boye yadda take ji a ranta ba.

Bahaushiya yar Gombe ta fantsama yanar gizo neman mijin aure
Bahaushiya yar Gombe ta fantsama yanar gizo neman mijin aure
Asali: Twitter

Salmerh wacce ta kasance ‘yar jihar Gombe, ta wallafa hotunanta guda biyu a shafin nata domin nuna wa mutane irin kyawun da Allah ya yi mata.

Shakka babu matashiyar na so ta dandani zuman da ke cikin aure sannan ta bar duniyar yan matanci.

Wallafar da ta yi ya sa mutane da dama yin sharhi inda suka dunga fadin albarkacin bakunansu.

Wasu daga cikin masu sharhin sun nuna ra’ayinsu na son mallakar budurwar a matsayin matarsu, cewa suma a kasuwa suke.

Har ta kai wani ya ma ajiye lambar wayarsa, inda ya bukaci da ta kira shi.

Wani mai amfani da shafin Twitter ya bukaci da ta duba halayya sosai domin tana da kyau da bai kamata ace bata da mashinshini ba.

KU KARANTA KUMA: Abin alfaharinmu: Harshen Hausa ya zamo yare mafi saurin yaduwa a duniya

A wani labari na daban, babban faston kasar Kenya, Fasto Godfrey Migwi, ya sanar da cewa ba zai sake daura aure ba matukar angon bai taba ganin amaryar ba babu kwalliya.

Faston ya ce dole ne ango ya ga fuskar amaryarsa ba tare da kwalliya ba na a kalla makonni uku kafin auren.

Ya kara da cewa, wannan ne babban dalilin da yasa aure ke mutuwa a wannan zamanin, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Migwi ya yi kira ga sauran masu coci da su bi ayarinsa domin rage yawaitar mutuwar aure da ya zama ruwan dare yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel