Buhari ya bada umarni a daina biyan kudin wuta da kai, a komawa na’ura

Buhari ya bada umarni a daina biyan kudin wuta da kai, a komawa na’ura

A wani jawabi da hukumar NERC ta fitar, ta musanya rahotannin da ke yawo na cewa an yi karin farashin kudin shan wutar lantarki a fadin Najeriya.

NERC ta yi karin haske game da rade-radin tashin farashin wutan, ta ce ba haka abin da ya ke ba, za a ga karin farashin shan wuta ne a bisa wasu sharuda.

Wadanda za su ga sauyi a kudin lantarki su ne wadanda ake ba wuta sosai, kuma duk da haka kafin nan sai kamfanonin raba wuta a kasar sun tuntubi jama’a.

“A duk yadda aka tafi, talakawa da marasa karfi a Najeriya ba za su gamu da wani kari ba. Inji hukumar.

NRC ta kara da cewa: “Saboda haka, ana ba kamfanonin DISCOs umarni su tattuna da mutane game da farashin shan wutan a kan wadannan sharuda:

“A tuntubi mutane, a yi magana da su cewa DISCO za ta rika ba su wuta na tsawon sa’o’i. A sa wa mutane na’urar awo, ba za a rika biyan kudi da kintace ba a wannan tsari. Wannan ya na nufin mutane ba za su fuskanci karin farashin da ya zarce abin da ake karba a hannun sauran makwabtansu ba.”

KU KARANTA: Motoci za su koma amfani da gas domin a rage shan man fetur – Minista

Buhari ya bada umarni a daina biyan kudin wuta da kai, a komawa na’ura
Buhari ya ce za a koma aiki da na'ura
Asali: Twitter

“Ko ga wadanda su ka cika wadannan sharuda, ba za ayi wa masu shan lantarkin da bai kai 50KW karin kudi ba."

"Mutanen da ba su samun wuta na akalla sa’a 12 a rana ba za su fuskanci karin farashi ba.”

“Bayan haka, shugaban kasa ya bada umarni a kawo shirin makala na’urar awo a ko ina a fadin kasar nan.”

Wannan ya na cikin yunkurin gwamnatin tarayya na ganin kamfanoni sun daina kintatar abin da mutane za su biya a matsayin kudin wutan wata.

Gwamnatin Buhari ta kuma yi lamuni ga masu shigo da na’urorin auna wuta, za a daina karbar harajin shigo da kaya ga duk wanda ya kawo wadannan na’urori daga ketare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel