Bayan shekaru 13: Gwamna Zulum zai gudanar da zaben kananan hukumomin Borno

Bayan shekaru 13: Gwamna Zulum zai gudanar da zaben kananan hukumomin Borno

- Za a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Borno cikin watan Nuwamba bayan shekaru goma sha uku

- Yawan hare-haren ta’addanci, wanda aka fara a 2009 ne ya yi sanadiyar dakatar da zaben kananan hukumomi a jihar

- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Borno (BOSIEC), Alhaji Abdu Usman, ya bayyana cewa an dauki matakan da suka kamata domin zaben kananan hukuma ya gudana a ranar 28 ga watan Nuwamba

A watan Nuwamban wannan shekarar, za a gudanar da zaben kananan hukumomi, wanda rabon da a yi su a jihar Borno tun a shekarar 2007.

Hauhawan hare-haren ta’addanci, wanda aka fara a 2009 ne ya yi sanadiyar dakatar da zaben kananan hukummomi a jihar.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Borno (BOSIEC), Alhaji Abdu Usman, ya bayyana a wani taron manema labarai a Maiduguri cewa an dauki matakan da suka kamata domin zaben kananan hukumomi ya gudana a ranar 28 ga watan Nuwamba.

Bayan shekaru 13: Gwamna Zulum zai gudanar da zaben kananan hukumomin Borno
Bayan shekaru 13: Gwamna Zulum zai gudanar da zaben kananan hukumomin Borno
Asali: Twitter

Usman ya ce: “An saka ranar 28 ga watan Nuwamban 2020, domin gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar. An shirya matakan da suka kamata tare da jerin tsare-tsaren zaben.”

A bisa ga jadawalin, hukumar ta mika takardar sanar da zaben a ranar 10 ga watan Maris kuma ya isa ga jam’iyyun siyasa a ranar 12 ga watan Maris.

Zabukan fidda ‘yan takara na jam’iyya zai gudana tsakanin 27 ga watan Agusta da kuma 21 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: A raba ni da matata Amina domin ta yi kokarin sanya mani guba – Magidanci ya sanar da kotu

Mika sunayen zababbun ‘yan takara daga jam’iyyu zai zo karshe a tsakanin 22 da 28 ga watan Satumba, da misalin 8:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a kullun.

An kuma shirya tantance ‘yan takara a tsakanin 9 da 15 ga watan Oktoba.

Shugaban hukumar zaben ya ce za a tura jami’an zabe da kayayyakin zabe tsakanin 25 da 27 ga watan Nuwamba yayinda kamfen zai tsaya a ranar 26 ga watan Nuwamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel