Yadda matata ta lalata kiran da nake na a bi Allah – Wani Fasto ga kotu
- Wani malamin addini, Adebayo Bamidele, ya roki kotun gargajiya da ke zama a Mapo, Ibadan, da ta rushe aurensa na shekaru 17 da matarsa Felicia
- Ya yi ikirarin cewa Felicia tana lalata masa harkoki da yin wasu zarge-zarge a kansa wanda ya sa mabiyansa suka gudu daga cocinsa
- Shugaban kotun, Ademola Odunade, ya rushe auren dunda bangarorin biyu basu da niyan ganin zaman lafiya a wanzu a tsakani
Wani malamin addini, Adebayo Bamidele, ya roki kotun gargajiya da ke zama a Mapo, Ibadan, da ta rushe aurensa na shekaru 17 da matarsa Felicia, kan hujjar cewa tana lalata masa harkoki.
Bamidele ya fada ma kotun a ranar Talata cewa matarsa na aikata abubuwan da ke lalata masa kiran da yake zuwa ga Ubangiji.
“Tana yi mun zarge-zarge masu lalata suna a gaban mabiyana.
“Ta mayar da ni mara aikin yi.
“Duk mabiya na sun bar coci na,” in ji shi.

Asali: Twitter
Faston ya ci gaba da fada ma kotun cewa wasu mambobin cocin sun nakada masa dukan tsiya biyo bayan zarge-zargen da Felicia ta yi a kansa.
“Felicia ta fada masu cewa ina amfani da bakaken aljanu da sihiri wajen kwashe masu arzikinsu.
“Sun yi mun mugun duka, sun yaga mun kayana.
“Har na kusa mutuwa.
“A yanzu tana ikirarin cewa cocin nata ne.
“Maganar gaskiya shine mun hada kudi wajen gina cocin, na rasa hanyar samuna saboda mugun nufinta a kaina,” in ji shi.
Da take amsa karar, Felicia ta bayyana cewa ta samar da N340,000 don kafa cocin.
Ta zargi Bamidele da yin harka da wata bazawara, cewa “tuni suka koma zama tare, dole ne ya dawo mun da kasona da na zuba.
“Muna da mambobi daga wurare daban-daban.
“Daga bisani sai na gano cewa yana juyani yadda ya so a zahiri da badini.
KU KARANTA KUMA: Ba ma rabon N45,000 a matsayin tallafin korona, in ji hukumar NCDC
“Wasu lokutan, yana bani asiri don na saka a karkashin matashina da dare, na gano cewa rayuwata ta sauya ba yadda take ba a baya,” in ji ta.
Shugaban kotun, Ademola Odunade, ya rushe auren dunda bangarorin biyu basu da niyan ganin zaman lafiya a wanzu a tsakani.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng