Kashe-kashen Kudancin Kaduna: Cikakken bayani kan ganawar El-Rufai da Sultan ya bayyana

Kashe-kashen Kudancin Kaduna: Cikakken bayani kan ganawar El-Rufai da Sultan ya bayyana

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cikakken jawabi kan ganawarsa da Sultan na Sokoto

- El-Rufai ya ce basaraken ya shawarce shi kan yadda zai tabbatar da maslaha maid ore a yayinda ake tsaka da hare-hare a Kudancin Kaduna

- An kuma tattaro cewa Sultan ya nuna goyon baya kan kokarin da ake amfani da su domin kawo zaman lafiya a Kaduna

Cikakken bayani kan ganawar Gwamna Nasir El-Rufai da Sultan na Sokoto, mai martaba Muhammad Sa’ad Abubakar III, a ranar Litinin, 24 ga watan Agusta, ya bayyana.

A cewar jaridar The Nation, tattaunawar da ya gudana cikin sirri a gidan Sir Kashim Ibrahim a babbar birnin jihar tsakanin El-Rufai da basaraken ya kasance a kan kashe-kashe da ake yi a Kudancin Kaduna.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar, Sultan ya dai ce kawai ya zo ziyartar dan’uwansa ne.

Kashe-kashen Kudancin Kaduna: Cikakken bayani kan ganawar El-Rufai da Sultan ya bayyana
Kashe-kashen Kudancin Kaduna: Cikakken bayani kan ganawar El-Rufai da Sultan ya bayyana Hoto: Gwamnatin Kaduna
Asali: Twitter

Sai dai kuma, El-Rufai ya bayyana cewa basaraken arewan ya zo Kaduna ne domin shawartarsa a kan yadda zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a Kudancin Kaduna biyo bayan hare-haren da ake kai wa yankin.

KU KARANTA KUMA: Ba ma rabon N45,000 a matsayin tallafin korona, in ji hukumar NCDC

A cewar gwamnan, Abubakar ya nuna farin ciki cewa addinai daban-daban da kungiyoyin kabilu a jihar ne ke bayar da dabarun wanzar da zaman lafiya a jihar.

Ya ci gaba da cewa basaraken ya basa shawarwari yayinda ya nuna goyon baya ga kokarin gwamnatin jihar wajen kawo zaman lafiya a jihar arewan.

Gwamnan ya yi addu’an cewa ziyarar Sultan zai zama mafarin zaman lafiya mai dorewa a Kudancin Kaduna.

A baya mun ji cewa kimanin sa'o'i 24 da ziyarar tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, zuwa wajen Gwamna Nasir El-Rufa'i, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya dira jihar Kaduna don kawo nasa ziyarar.

Mai alfarma sarkin Musulmi ya dira gidan gwamnatin Kaduna misalin karfe 12: 20 na rana a yau Litinin, 24 ga Agusta, 2020.

Ya samu tarba daga sakataren gwamnatin jihar, Balarabe Abbas; shugaban ma'aikatan El-Rufa'i, Muhammad Sani Dattijo; da kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel