Yadda aka yi garkuwa da mutane akalla 7 a ‘yan kwanaki a Garin Shika

Yadda aka yi garkuwa da mutane akalla 7 a ‘yan kwanaki a Garin Shika

- Rahotanni sun tabbatar da cewa an addabi yankin Giwa da garkuwa da mutane

- A ‘yan kwanakin nan, an yi garkuwa da mutane da-dama a cikin garin Shika

- Daga cikin wadanda aka sace har da wata yarinya da ta zo ziyarar ta’aziyya

A daidai lokacin da ake fama da kashe-kashe a yankin kudancin Kaduna, mutanen karamar hukumar Giwa su na kukan garkuwa da mutane.

Legin.ng Hausa ta samu labarin irin satar da mutanen da ake yi a yankin Giwa, ana tsare Bayin Allah har sai ‘yanuwa ko abokansu sun biya kudin fansa.

A ranar 11 ga watan Agustan nan ne masu garkuwa da mutane su ka shiga wani kauye da ake kira Tashar Zomo, a garin Shika, su ka sace mutane hudu.

Wani Bawan Allah mazaunin wannan yanki ya shaidawa jaridar Legit.ng cewa har yanzu wadannan mutane da aka sace, su na hannun ‘yan bindiga.

KU KARANTA: Rikici ya kaure tsakanin Jami’ai da IPOB, an rasa rayuka 23

Yadda aka yi garkuwa da mutane akalla 7 a ‘yan kwanaki a Garin Shika
Ana fama da garkuwa da mutane a Kaduna
Asali: Twitter

A lokacin da ake kukan wannan lamari kuma sai aka ji ‘yan bindigan sun aukawa garin Tawatsu, sun sace ‘diyar wani Bawan Allah a ranar Larabar da ta wuce.

Majiyar ta ce wannan yarinya da aka yi garkuwa da ita, ta zo garin ne daga jihar Kano domin yi wa ‘yanuwanta ta’aziyyar rasuwa da aka yi masu kwanakin baya.

Har ila yau, a karshen makon da ya gabata aka wayi gari a garin Shika da mummunan labarin sace wasu mutum biyu. An yi wannan ne a unguwar Hayin Madaki.

Duk wannan abu ya auku ne a karamar hukumar Giwa a Kaduna, a cikin kasa da makonni biyu. Tun ba yau ba ana fama da matsalar rashin tsaro a yankin mai iyaka da Katsina.

Wani Bawan Allah da ke zaune a karamar hukumar Giwa, ya shaida mana cewa satar mutanen da ake yi a Shika da kewaye ya jefa al’ummar yankin cikin halin firgici.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel