Laifin Gwamnatin baya ne, babu hannun Shugaba Buhari a tsadar kayan abinci – Badaru

Laifin Gwamnatin baya ne, babu hannun Shugaba Buhari a tsadar kayan abinci – Badaru

Gwamnan jihar Jigawa, Mohammadu Badaru Abubakar, ya ce mutanen Najeriya su daina zargin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan halin da aka shiga yau.

Yayin da ya ke yabawa kokarin Isa Ali Ibrahim Pantami, Mohammadu Badaru Abubakar ya ce matsalar da kasar ta samu shi ne ta dogara ne da shigo da kaya daga kasashen waje.

Mai girma Ministan sadawara, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya zo jihar Jigawa ne domin kaddamar da wasu ayyuka da ma’aikatun NITDA da NCC su ka yi a karkashin ma’aikatarsa.

Da ya ke jawabi, gwamnan na Jigawa ya yabawa ministan, ya kuma kare shugaban kasa Buhari, ya ce babu hannunsa a tsadar da abinci da sauran kayan amfani su ka yi a kasuwa.

“A shekaru biyar da su ka wuce na gwamnatin baya, an saida gangar mai a kan Dala 100, a shekaru biyar na gwamnatinmu, kusan ana saida mai ne a $50.” Inji Badaru Abubakar.

“Ma’aikatar harkokin jiragen sama ta kaddamar da ayyuka 150 a shekaru hudu, kuma ana kan wasu. Kusan haka abin da ya ke a sauran ma’aikatu, da rabin kudin da ake samu.”

KU KARANTA: 'Yan Arewa 4 da su ke goyon bayan mulki ya koma yankin Kudu a 2023

Laifin Gwamnatin baya ne, babu hannun Shugaba Buhari a tsadar kayan abinci – Badaru
Badaru ya na ganin Buhari ya cancanci jinjina
Asali: Twitter

Gwamnan ya ce: “Da akalla rabin kudin da Muhammadu Buhari ya samu, mun yi aiki sosai.”

Gwamnan ya ke cewa: “Fam dala biliyan 29 ne a cikin asusun kudin kasar waje a lokacin da m ka zo. Dole mu ga laifin shugabannin baya, sun san farashin mai ba zai daure ba. ”

“Mu na ganin laifin Buhari, amma ba shi ya jawo farashin mai ya sauka ba. Mun kasance mu na shigo da kaya da Dala saboda shugabannin baya sun sa mu na kawo komai daga waje.”

Gwamnan ya cigaba da sukar gwamnatin PDP, “Sun samu damar daidaita kudin kasa, amma ba su adana komai don gobe ba, amma su na fitowa su na zargin Buhari a kan tsadar kaya.”

“Duk wani mai adalci ya sa Buhari ya cika alkawuransa, ya kuma cancanci yabonmu. Mun yi kokari sosai.” Badaru ya ce ba Buhari ya kashe zomon ba, rataya aka ba shi.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel