Za a bude makarantun jami’a da sauransu kwanan nan, in ji minista

Za a bude makarantun jami’a da sauransu kwanan nan, in ji minista

Karamin ministan ilimi, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba, a ranar Litinin, ya ba daliban Najeriya tabbacin cewa za a bude makarantun gaba da sakandare a fadin kasar kwanan nan.

Koda dai bai bayar da ainahin ranar budewar ba, ya bukaci dalibai da su daina zanga-zanga.

Ya bayyana cewa ma’aikatar na aiki domin samun rahoto daga hukumar makarantun Jami’a (NUC) da sauran hukumomi na makarantun gaba da sakandare daban daban.

Bayan samun rahoton za ta gabatar da su ga kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da annobar korona domin dubawa, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Nwajiuba, wanda ya bayyana hakan yayinda yake amsa tambayoyi a taron PTF a Abuja, ya kara da cewar ma’aikatar ta samu kira daga jami’o’i masu zaman kansu da jami’o’in gwamnati don sake bude makarantun kasar.

Za a bude makarantun jami’a da sauransu kwanan nan, in ji minista
Za a bude makarantun jami’a da sauransu kwanan nan, in ji minista Hoto: Guardian
Asali: UGC

“Akwai ci gaba sosai, sai dai, jagorancin da aka bamu wanda muke samun rahoto daga makarantu da dama a yanzu haka sun hada da wasu kayayyaki da ake bukatar ku shirya kuma bama son cuwa-cuwa, muna so mu gani a kasa sannan Za mu koma domin ganin ko mutane sun bi abubuwan da ake bukata.

“Da safiyar nan, ni da ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, babban sakataren NUC da sakataren din din din mun gana sannan muna a kan haka tun safe. Mun duba bayanai daga kimanin jami’o’i 78 zuwa yanzu sannan mafi akasarinsu jami’o’i na kudi ne wadanda suka ce sun shirya dawowa. Muna kuma da bayanai daga jami’o’i jiha guda 50 kuma muna aiki domin tabbatar da cewar kowa ya shirya.”

Ya kara da cewa: “a lokacin da ake dukka wadannan, za mu gabatar da su a gaban PTF domin jami’an kwamitin su sake dubawa don bayar da izinin bude makarantu.

KU KARANTA KUMA: Najeriya na neman hakkin danta, Ibrahim Khaleel Bello wanda aka kashe a kasar Cyprus

“Muna da yakinin cewa lokaci ya kusa, amma bama son mu dunga chanje chanjen rana, kawai muna da yakini.

“Ina bukatar dalibanmu da suka yi hakuri sosai da su kara mana dan lokaci kadan. Ya zama dole a dakatar da zanga-zangan. Babu wani abun yin zanga-zanga a kai. Muna kan tattaunawa da ASUU dari bisa dari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel