N20, 000 da za a biya Ma’aikatan da za a dauka ya saba dokar kasa – Hon. Chinda
Mun ji cewa ‘yan jam’iyyar PDP da ke majalisa sun fito su na yi wa gwamnatin tarayyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke jagoranta barazana.
Jaridar Punch ta rahoto cewa ‘yan adawa a majalisar wakilan tarayya sun sha alwashin shiga kotu da karamin ministan kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo.
‘Yan hamayyar za su kai ministan gaban Alkali ne saboda raina majalisa da ya yi, musamman wajen shirin da ya fito da shi na daukar ma’aikata na musamman.
‘Yan PDP da ke majalisar tarayya sun ce sun janye kansu daga wannan shiri na gwamnati, kuma sun yi kira ga abokan aikinsu, su yi watsi da takardun da aka aiko masu.
Wadannan ‘yan majalisa sun zargi Festus Keyamo SAN da shugabannin ma’aikatar NDE da rashin ganin kimar majalisar tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Buhari.
Lamarin har ta kai ‘yan majalisar su na da-na-sanin sa hannu wajen amincewa da Naira biliyan 52 da aka ware domin wannan aiki a kundin kasafin kudin shekarar bana.
KU KARANTA: Mai ba Shugaban kasa shawara ya kare Aisha Buhari
Bayan haka, ‘yan majalisar sun ce N20, 000 da za a biya wadannan ma'aikata 774, 000 da za a dauka aiki ya saba doka, domin kuwa shirin ya ci karo da dokar albashi ta kasa.
Shugaban wannan tafiya, Honarabul Kingsley Chinda ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a ranar Litinin, 24 ga watan Agusta, 2020, ya na mai sukar tsarin.
Kingsley Chinda ya ke cewa za su maka gwamnati a gaban Alkali a game da hakkinsu da aka taka. Chinda ya zargi gwamnati da kawo siyasa a cikin harkar daukar aikin.
“'Yan PDP sun yanke hukuncin amfani da damar da majalisa da shari’a ta bada wadanda su ka hada har da zuwa kotu domin shawo kan shiga huruminmu da keta hakkinmu.”
Chinda ya ce: “Watsi da karamin minista ya ke yi da bangaren majalisa na gwamnati wadanda mutanen Najeriya su ka zaba da kuma amincewar shugaban kasa a kaikaice wajen bada umarnin cigaba da wannan aiki duk da kura-kuren da ke ciki, ya nuna gwamnatin Buhari ba ta damu da bin doka, da tsarin mulki ba, kuma babu abin da ya dame ta da halin da mutane su ke ciki.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng