Na kan ji kunya idan na ga wasu ‘yan majalisa na bacci a zauren majalisar – Babban alkalin tarayya
- Ishaq Bello, babban lauyan kotun FCT ya yi tsokai a kan cece-kuce da ke kewaye da baccin ‘yan majalisa a lokacin tattaunawa a zauren malisar
- Bello ya ce ya kan sha kunya a duk lokacin da ya ga 'yan majalisar na bacci a zauren ba tare da bayar da kowani gudunmawa ba a lokacin zantawa
- Ya bayyana cewa akwai bukatar matasa masu jini a jika su fito su kawo canjin da ake bukata a fadin kasar
Babban alkalin babbar kotun birnin tarayya (FCT), Ishaq Bello ya yi tsokai a kan cece-kuce da ke kewaye da baccin ‘yan majalisa a lokacin zaman al’ada a zauren majalisar.
Bello ya bayar da tabbacin cewa akwai bukatar matasa masu jini a jika su fito su kawo canjin da ake bukata a fadin kasar.
Ya bayyana hakan ne a wani taron kara ma juna sani da aka shirya ma lauyoyi masu tasowa a ranar Litinin, 24 ga watan Agusta, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Asali: Facebook
Babban alkalin ya bayyana cewa ya kan sha kunya a duk lokacin da ya ga ‘yan majalisa na bacci a yayin zamansu.
KU KARANTA KUMA: Najeriya na neman hakkin danta, Ibrahim Khaleel Bello wanda aka kashe a kasar Cyprus
Ya ce: “Idan na ga mutane masu yawan shekaru na bacci a majalisar dattawa ko majalisar wakilai, ba tare da suna bayar da kowani irin gudunmawa ba alhalin suna da matasa masu jini a jika a mazabunsu da za su inganta, na kan ji kunya.”
Kan rikicin da ya kunno kai a kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), biyo bayan zaben Olumide Akpata, wanda ba babban lauya (SAN) bane a matsayin shugabanta, Bello ya bukaci manyan lauyoyi da su amshi sakamakon zaben hannu bibbiyu.
A wani labari na daban, majalisar Wakilai ta yi barazanar yin karar Ministan Niger Delta Godswill Akpabio a kotu kan ikirarin da ya yi na cewa kaso mai yawa cikin kwangilolin hukumar NDDC, yan majalisan ne aka bawa.
Ministan ya yi wannan ikirarin ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar da aka kafa domin duba kudaden da ake kashewa a hukumar ta NDDC da ake ganin ya wuce hankali.
Daily Trust ta ruwaito cewa Majalisar, a zaman ta na ranar Talata, ta kallubalanci ministan ya wallafa sunayen yan majalisar da ya yi ikirarin sun karbi kwangilar a NDDC.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng