“A dalilin na ki jefa Magu a cikin matsala, Ministan shari’a ya sa aka kama ni”
Wani Lauya, Victor Giwa, ya ce ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya sa a tsare shi ne a dalilin Ibrahim Magu.
Victor Giwa ya ce saboda ya ki jefa tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu a cikin matsala ne Abubakar Malami SAN ya bada umarnin a cafke shi.
Giwa ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi bayan ya fito daga hannun hukumar EFCC.
An tsare lauyan tare da wata Fatima Hassan a makon da ya gabata, bayan sun hallara a gaban kwamitin Ayo Salami da ke binciken ayyukan Ibrahim Magu a EFCC.
Wani mutumi mai suna Donald Wokoma wanda ya yi aiki da lauyan, ya shaidawa kwamitin an rufe masa asusun bakinsa bisa umarnin Magu lokacin ya na rike da hukumar.
Kamar yadda jaridar Punch ta ftar da rahoto, a dalilin haka ne Donald Wokoma ya dauko hayar Victor Giwa domin ya kai shigar masa da karar hukumar EFCC a kotu.
Mista Wokoma wanda ya taba aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce ya yi nasara a kotu, har aka bada umarni a bude masa asusunsa.
KU KARANTA: Magu zai soma gabatar da hujjojin kare kan shi a gaban kwamiti
Amma a cewarsa, an bukaci a biya cin hancin Naira miliyan 75 kafin ayi wa kotu biyayya. Giwa ya fadawa Wokoma cewa Magu ya nemi a biya cin hanci ta hannun wani yaronsa.
Domin tabbatar da zargin da ya ke yi, Wokoma ya gabatar da sakonnin waya da faifen sautin tattaunawarsa da Victor Giwa inda aka ji ya na masa maganar neman cin hanci.
Lokacin da Giwa ya bayyana gaban kwamitin, ya karyata wadannan zargi na neman bada cin hanci, ya ce Magu mutumin kwarai ne, ana cikin haka jami’an tsaro su ka kama shi.
Giwa ya zargi Abubakar Malami SAN da kitsa kama shi da aka yi, ya ce Ministan ya na amfani da Wokoma da su ka yi aiki tare a baya wajen yin ram da shi da Lauya Hassan.
Lauyan ya ce abin da ya jawo masa matsala tare da Fatima Hassan shi ne kin ambatar abin da zai jefa Ibrahim Magu a matsala, ya ce ba wai sun aikata wani laifi ba ne.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng